Tarihin Fatima Zahra [a.s]



2. Allah ya titita ƙi a kan duKKan natma,
Da falalar wanda ake wa wahayi.

3. Allah ya aurar miki da saurayi mafifici,
Jna nufin Aliyu mafi alherin rayayyu.

4. Ku jera makwabtana tare da ita

Ita ce mai karimci 'yar Shugaban halittu.

Bayan an kai ta sai Manzo ya ce a kawo masa kwarya da ruwa, sai ya yi addua a ciki ya yayyafa mata a kai da jiki. Shi ma Aliyu (AS) ya yi masa haka. Sannan ya umurce su da su yi alwala. Sai Fatima ta fashe da kuka. Sai ya ce me ya sa ki kuka? Ashe ban aura miki mafi hakurinsu ba? Mafi iliminsu. Sai ya fito zuwa kofar dakin sai ya ce "Allah ya tsarkake ku ya tsarkake iyalanku. Ni makiyin makiyinku ne, masoyin masoyinku ne. Na bai wa Allah ajiyarku. Na bai wa Allah amanarku." Daga nan sai ya jawo kofar. Sai ya fito ya salami "yan buki baki daya.

Bayan ya fito kofar sai ya ga wata mace. Sai ya ce "Wacece''" Sai ta ce ita ce Asma'u. Sai ya ce "Ashe ban sallame ku ba9" Sai ta ce "'Haka ne ya Manzon Allah. Ba ina nufin sabawa bane. sai dai alkawari ne tsakani na da Khadija (AS) lokacin da za ta yi wafati. Sai ta kwashe labarin gaba daya ta ba shi. kamar yadda muka yi bayani a can baya. Manzo na jin haka. sai hayyaye suka zubo masa. Sai ya ce "Ni ma don irin wannan na tsaya har zuwa yanzu."

ZIYARTAR MANZO (SAAW) GIDAN NANA FATIMA (AS)

Washegarin bukin da safe. Manzo ya ziyarci Nana da ntijintsL ya tafi musu da nono don tsaraba. Bayan ya ba su nonun sun sha. sai ya tambayi Imam ya ce "Yaya iyalinka Sai Imam ya ce "Na same ta mai taimako a kan yi wa Allah daa." Sannan ya juya ya tambaye ta "Yaya mijinki r"Sai ta ce "Na same shi mafi alheri daga cikin mazaje. 3

Daga nan sai Manzo bai kuma zuwa ba sai bayan kwana uku. Sai ya tambaye ta "Yaya gida?.Yaya mijinki?" Sai ta ce yana nan lafiya cikin alheri. Sai dai wasu daga cikin matan Kuraishu sun shigo sun ce min wai ka aura min da fakiri, wanda ba shi da komai." Sai Manzo ya ce: "Ya diyata, babanki da mijinki ba fakirai bane An miko min taskokin da ke cikin kasa baki daya na ki karba, na zabi abin da ke gurin Allah.

"Ya diyata babu wani abin alherin da zan miki kamar in aurar miki da wanda ya riga su musulunta, mafi iliminsu, sannan yafi hakurinsu Ya diyata lallai Allah Mabuwayi da daukaka ya duba cikin halittunsa baki daya sai ya zabi mutum biyu, daya Mahaifinki, daya Mijinki!

"Ya diyata madalla da miji, mijinki, kada ki saba masa kan wani aramari." Sannan sai ya kirawo Imamya ce masa "Ka shiga gidanka ka zauna tare da matarka, ka dinga tausasa mata. Lallai Fatima tsoka ce daga gare ni. yana bakanta min duk abin da ya bakanta mata. Yakan faranta min duk abin da ya faranta mata. Na bai wa Allah ajiyarku, na kuma bai wa Allah amanarku."



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next