Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Lokacin da Manzo (SAW) ya tsaya a Khaibar bayan ya ci su da yaki tsawon kwana uku. sai Yahudawan Fadak suka aiko mishi a kan a yi sulhu don kar ya iso gare su. a kan sun ba shi rabin gonar Fadak da abin da ke cikinta na dabinnai da sauran "yayan itace masu yawan gaske Bayan nan sai Allah (swt) ya saukar da wahayi a kan wannan gonar (Fadak) ya bai wa Manzo shi kadai, mallakar kansa inda yake cewa: "Abin da Allah ya sanya ganima ga Manzonsa daga mutanen kauyokan nan. to na Allahne. kuma na Manzonsa ne..."

Wannan gona ta kasance a hannun Manzo mallakarsa yana sarrafa gonar da abin da ake samu ta wajen taimaka wa Banu Hashim. fakirai da miskinan Madina An yi kiyasi a kan cewa akan samu misalin kamar dinare dubu Ashirin da hudu zuwa dubu sabain (N94.()8().OOO-274.400.000) ashekara.

Bayan da Allah (swt) ya saukar da ayar da take cewa: "Ka bai wa makusanta hakkinsu." Sai Manzo ya kira Fatima (as) ya ba ta wannan gonar kyauta.

Jalaluddin Suyudi ya ruwaito cikin littafinsa Durrul Mansur, juzu'i na hudu, shafi na 177 yana cewa: "An ruwaito daga Abi Sa'idul Khuduri yana cewa: Lokactn da aka saukar da ayar da Allah (swt) yake cewa "Ka bai wa makusanta hakkinsu." Manzo nan take ya mwatar da abin da Allah ya umurce shi, ya kira Fatima ya ba ta gonar Fadak kyauta."

An ruwaito daga Aliyn Ibn Abi Talib (as) yana cewa "Manzo ya bai wa Fatima (as) gonar Fadak kyauta *

An ruwaito daga Adiya yana cewa: "Lokacin da ayar da Allah (swt) ke cewa: "Ka bai wa makusanta hakkinsu.".., Manzo ya kira Fatima (as) ya ba ta gonan Fadak kyauta. Wannan hadisin da ke bawanar da cewa Manzo ya bai wa Fatima (as) Fadak kyauta "Mutawarin" hadisi ne, wanda malaman sunni da shi'a suka ruwaito shi. Don haka ba za mu tsawaita ba. sai dai mai karata yana iya bmcikawa don amfanin kansa. GWAMNATI TA AMSHE FADAK

Bayan kwana gotna da kaftiwaT gwamnati. sai Abubakar ya aika da Wakilinsa a kan ya je ya tashi Wakilin Fatima (as) a Fadak. ya ci gaba da rikewa karkashin hukuma Fatima (as) tana gida. sai ga Wakilinta hankalinsa a tashe. ya ba ta labarm duk abin da ya faru. Ko da ta ji haka. sai abin ya ba ta mamaki. ya bawana gare ta a kan cewan lallai akwai abin da ake nufi Nana Fatima tana da hanyoyi uku na kafa hujja a kan Fadak nata ne a shanar Musulunci: Fadak yana hannunta ne. Wakilinta ne a ciki a matsayin shaidar da ke nuna mallakarta ne. A Musulunci ba za a karba a hannunta ba. sai an zo da shaidu wadanda suka yi shaida a kan ba nata bane. ko kuma a sanya ta ta yi rantsuwa a kan nata ne. Akwai shedu wadanda suka tabbatar da cewa Manzo ya ba ta kyauta. Tana da lkon ta gaji gona daga Mahaifinta kamar yadda Allah ya yi umurni cikin Kur'ani.

Halbi ya ruwaito a cikin littafin siransa. juzui na uku. shafi na 39. yana cewa: "Fatima ta zo gurin Abubakar bayan wafatin Manzon Allah (saw) tana cewa: Lallai Fadak mallakar Mahaifina ne. sannan ya ba ni kyauta tun yana raye." Sai Abubakar ya yi mkarin haka. Sai ya ce ta jo ta zo da shaidu Sai Aliyu ya yi mata shaida a kan haka Sai Abubakar ya ce sai karo waiii. sai    sai ta Ummi Aiman . sai  ya ce bai yiwuwa ya  ba ta a kan shedar namiji daya da mace daya tak.?'

Ga wata ruwayar kuwa, lokacin da Ummi Aiman ta zo, kafin ta yi shaida sai da ta ce: "Ba zan yi shaida ba ya Abubakar, sai na kafa maka hujja a kaina guda daya. Sai ta ce: Ina gama ka da Allah ka taba jin Manzo ya ce Ummu Aiman mace ce daga cikin matan Aljanna? Sai ya ce ' na taba ji' Sai ta ce: "Na rantse da Allah Mai girma da buwaya lokacin da Allah ya yi wa Manzo wahayi da ayar da yake cewa "Ka bai wa makusanta hakkinsu..." Manzo ya kira Fatima ya ba ta gonar Fadak kyauta. Daga nan Abubakar ya dauko takarda ya rubuta wa Fatima cewa lallai Fadak nata ne. Umar na shigowa, sai ya tambayi abin da ke faruwa. Da aka ba shi labari, sai ya kwace takardar ya yaga. Fatima ta fita ta koma gida tana kuka.

"Bayan nan sai Aliyu (as) ya dawo masallaci. sai ya tarar da Abubakar sai ya tambaye shi don mc ya hana Fatima gadonta alhali Mahalfinta ya ba ta tun yana raye? Sai ya ce: Sai ta zo da shedu zan ba ta. amma in ba haka ba ba zan ba ta ba' Sai Aliyu ya ce: Me ya sa kake mana hukunci inn wannan? Yanzu idan na yi ikirann wani abu nawa ne wanda yake hannun musulmi. wane ne za ka ce ya kawo sheda? Sai ya ce kai (yana nufin Aliyu). Sai ya ce To don me za ka ce Fatima ta kawo sheda a kan abin da yake hannunta?" Sai Abubakar ya yi shuru. Daga nan sai ya ce 'Wannan ba hujja banc sai kun zo da shcdu Adalai kafin in ba ku." Sai Aliyu ya ce masa *Ayar da Allah yake cewa. Allah yaiui nufin ya tafiyar da duuda ne daga gare ku iyalan gidan Manzo, sunnan ya tsarkake ku tsarkakeua," a kan su wa ta sauka'.' Sai ya ce a kanku .. har zuwa karshe. kamar yadda muka yi bayani a can baya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next