Tarihin Fatima Zahra [a.s]An ruwaito daga Jabir Ibn Abdullahi (ra) yana cewa Wani Balaraben kauye ya zo gun Manzo don ya musulunta. Sai Manzo ya ce 'Ka ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kunia Annabi Muhammad bawansa ne. Manzonsa." Bayan ya fada. sai ya ce "Nawa zan biya ka? Sai Manzo ya ce "'Ba abin da za ka biya sai dai nuna kauna ga makusanta." Sai ya ce "Makusantana ko makusantanka" Sai Manzo ya ce "Makusantana (halan gidan Manzo)" Sai ya ce "'Miko hannu in yi maka baia. sannan kuma Allah ya la'anci duk wani wanda ba ya kaunar iyalan gidanka." Sai Manzo ya ce "Amin." Imam Shafri yana cewa cikin wake: Iyalan gidan Manzo son ku, Wajibi ne cikin Kur'an Allah ya saukar. Ya ishe ku abin alfahari da matsayi Wanda bai muku salati cikin salla ba babu sallarsa. NANA FATIMA (AS) DA WAHALHALUN GIDA Nana Fatima (AS) ita ce mafi sanin darajar aure da abin da ke cikinsa, na yardar Allah (SWT) da fushinsa. Kowane aFamari na zaman aure ba mai boyuwa bane gare ta. Ta kasance a cikin gidan mijinta kodayaushe mai neman yardar Allah cikin hakkokin da ke kanta na zaman aure. Tana kulawa da yara wajen tarbiyya da ilmantarwa. Tana kulawa da aikace-aikacen gida baki daya kamar; daka. surfe. wanki, wanke-wanke, shara. hura wuta. debo rmya, dss. Bayan nan kuma a kullum matan Madina sukan zo gun ta don daukar karatu da koyon addini. Sai ya zatna kodayaushe tana cikin kurarren lokaci na yin aikace-aikacen gidanta. Idan sun netni su taimaka tnata sai ta ki yarda. Dukkarun rayuyyar Fatima (AS) ta yi su ne cikinjuriya da wahalhalu. daga wannan sai wannan har takomaga Ubangijinta ta Madaukakin Sarki. An ruwaito daga Imam Aliyu (AS) yana fada ma wani daga ciki Bani Sa'ad yana cewa: "In ba ka labann zamantakewarmu da Fatima? Ni ke tare lta alhali lta ce mafi soyuwa ga Maiizo. Ta kasance tana dauko niwa a tulu har sai da ya yi alama a kirjinta. tana yin mka da dutsen nika har sai da hannunta ya daye. tana share gida har sai da tufafinta ya nne saboda kura. tana hura yyuta har sai da tufafinta ya dafe saboda hayaki. Wannan ya haifar tnata da tsanani mai yawa. Sai na ce niata da za ki je gurin Manzo ki tambaye shi baiwa wacce za ta dinga taya ki aiki. da kin sami saukin wadannan wahalhalun. "Koda ta je gurin Manzo sai ta tarar da jama'a. sai kunya ta hana ta. sai ta juyo ta dawo. Manzo ya fahimci cewa akwai abin da ke tafe da ita. Washegan sai ya zo da safe. Ya tambaye ta mene ne bukatarta Sai ta yi shim. Da na ga zai juya ba ta fada ba. sai na ce. Ya Manzo Allah wahalhalu ne na gida suka yi mata yawa shi ne ta zo don ta sami baiwar da za ta dinga taimaka mata. "Daga nan sai Manzo ya ce: Ba na sanar da ku abin da ya fi baiwaaheri ba? Idan zaku kwanta ku yi tasbihi sau 33, hamdala sau 33,kabbara sau sau 34 a karshe; ya zama dari kenan, amma a mizani dubu rie. Sai ta ce ta yarda da Allah da Manzonsa cikin duk abin da suka hukunta." Ga wata ruwayar kuwa shi ne: Lokacin da ta fadi bukatarta sai Manzo ya fashe da kuka. Sai ya ce "Ya Fatima na rantse da wanda ya tayar da ni da gaskiya, a masallaci akwai mutane 400, wadanda ba su da cin yau bare na gobe, ba suturan sawa. Ya Fatima ni ba na burin wata baiwa ta zq ta tafi da ladar da kike samu na aikace-aikacen gida." Sannan ya sanar da ita tasbihin ake yi bayan kowace salla. Ana kiran sa tasbihin Zahra. Wata rana Manzo ya shigo gurin Imam tafe da Fatima (AS) sai ya gan su suna nika. Sai ya ce "Wanene daga cikinku zan taimakawa?" Sai Imam ya ce "Ka taimaki Fatima don na ga ta gaji." Sai Manzo ya ce "Taso diyata in taimaka tniki."
|