Tarihin Fatima Zahra [a.s]



A cikin wannan yanayin ne. daga karshe Manzo (as) ya auro Saudatu. Awannan lokacin Fatima (as) tana da shekaru takwas a duniya. Daga nan kuma sai Allah (swt) ya umurci Mahaifinta da hijira zuwa Madina.

HIJIRA ZUWA MADINA

Lokacin da abubuwa suka yi tsanani bayan wafatin Khadija (as) da Abu Talib (as) Manzo yayi hijirazuwa Madinabayan farada'awarsada shekara 13 Lokacin da Manzo yayi nufin hijira ya sanya Imam Aliyu ya kwanta a gadonsa a wannan daren bayan samarin Kuraishawa wajen 40 karfafa sun kewaye gidansa suna ta fadar bakaken maganganu na cin mutunci da izgilanci. Fatima (as) idonta biyu duk tanaji. tanatunanin yau kuma wane mn bakin ciki za ta gani' Wai har ya zuwa yaushe ne wadannan tashin hankulan za su kare.-na jiya bai kai na yau ba. na yau bai kai na gobc ba.

Ko da Manzo ya gama yi wa Imam Aliyu (as) bayani a kan in gari ya wayc ya mika kayan da aka ba shi (Manzo) ajiya ga masu shi. sai Allah (swt) ya saukar wa wadannan yan ta'addan barci mai nauyi har Manzo ya zo ya yyuce ta gabansu ya zuwa kogon Hira. Daga nan kuma ya kama hanya zuwa Madina Bayan gari ya yyaye Imam Aliyu (as) ya taso daga Makka zuwa Madina tare da Fatima Zahara (as). Fatima binti Asad (Mahaifiyar Aliyu), Fatima binti Hamza da wasu matan musulmi.

Abu Wakid ya kasance shi ke jan tawagar, sai yana ta faman sauri sosai. Ko da Imam Aliyu (as) tambaye shi me ya ga yake wannan saurin. ya yi a hankali tnana saboda masu rauni? Sai ya ce mishi ai yana tsoro ne kada makiya su riske su su kama su. Sai Imam Aliyu (as) ya ce "Ba abirt da zai same mu har mu isa Madina. I-Jaka Manzo ya gaya min."

Suna cikin tafiya sun kusa da wani guri wanda ake kira DAJNAN sai wasu kafirai takwas suka riske su a kan su^koma da su Makka don su wulakanta su. Amma ina, ayari ne wanda ya hado da Aliyu mazan gaba, ki kafiri, kashe kafiri. gaba da maki salla, AHyti rana wacce tayo garji. Ko da ya zaro takobinsa ya tunkare su sai suka fashe kowa ya ranta a na kare. Manzo ya yada zango ne a wani yyuri wanda ake kira KUBA har tsawon kwana 12. yana jiran su Fatima (as) da Imam Aliyai (as) kafin ya shiga garin Madina. Don ya ce ba zai iya shiga garin Madina ba ba tare da su ba. Mutanen Madina sun dade suna sauraron zuwan Manzon Allah (saw). Ko da isowarsa sai suka fito kwansu da fcwarkwatarsu don tarbar Fiyayyen halittu da diyarsa Fatima (as). Shugabar matan duniya baki daya. suna raira wake suna buga mandiri Daga nan sai kowannensu yana kokarin Manzo ya sauka a gidansa bayan ya y'i fenti mai kyau da gyarc-gyare. Manzo ya ce musu su kyale Taguw arsa ta tafi. duk inda ta tsaya. to nan ne Allah (swt) ya nufe shi da sauka. Jim kadan sai Taguwar ta tsaya a kofar gidan Abu Ayub al-Ansan.

Manzo ya sauka a gidan Abu Ayub al-Ansari a Unguwar Banu Najjar. Manzo ya zabi kasan gidan saboda samun sauki ga masu ziyara. shi kuma Ayub al-Ansari yana sama. amma ya damu kwarai don ya yi kokann Manzo ya hau sama amma Manzo ya ki. Wannan ya sa matarsa ba ta shara ko wanke-wanke sai darc ya yi nisa gudun kar su dami Manzo

Bayan nan sai Manzo ya sa aka gina masallacinsa da dakuna uku don amfaninsa da iyalansa. Daya na Saudatu. daya na A'isha. sannan kuma daya na "yarsa Fatima (as). wanda mafi yawancin lokaci yaria' dakin yana debe mata kewa. karantarwa da sauran makamancin haka. Mafiya yawanci a wannan dakin Mala'ika Jibrilu yakc zo masa da wahayi. ita kuma Fatima (as) tana kallo. Shi kuwa Imam Aliyu (as) ya sauka ne a gidan Mu'azu Ibn Nuuman Al'ansari.10

KASHI NA BIYU

RAYUWAR NANA DA MAHAIFINTA A MADINA

Kamar yadda muka yi dan bayani a baya cewa Manzo ya gina gida mai dakuna uku tare da masallacinsa guri guda. Kuma ya kasance mafi yawancin lokaci yana tare da yarsa Nana. Wannan ya sa Nana ta fuskanci matsaloli wanda ya zamo mata jarrabawa daga matan Mahaifinta.

Ta kasance ita ce mafi soymya a gare shi. Ita ce kwalliyar zuciyarsa. kai kamar yadda yake fadi ita ce ruhinsa. wanda ke tsakanin kirjinsa. Irin wannan son da kusanci na rabbanhya da irfaniyya ya haifar da hassada a tsakaninta da sauran matan Mahaifinta. Wanda har ba sa iya danne shi sai sun bayyana ta wajen gayawa Nana (AS) maganganun da ba su dace ba da daukar mataki a kanta. yyanda wannan ya zama ci gaba da jarab^ar da Allah ya dinga jero mata tun haihuwarta.

Allama Majlisi ya ruwaito cewa "An samo daga Baban Abdullahi (Assadik (AS) yana cewa wata rana Manzo ya shigo gida sai ya ji tashin mun a ko da ya lura sai ya ga Aisha ta tasa Nana (AS) a gaba tana ta mata fada A ciki tana cewa: "Duk wannan gani-gani da kike mana kina mana ne don tunanin Mahaifiyarki ta fi mu ne. to da-me ta fi mu'.' Ita ba komai bace lllakamar mu. Ko da Manzo ya ji haka sai ya taho gun. Da Nana (AS) ta ga ya iso. sai ta fashe da kuka. Sai ya tambayc ta me ya faru ne' Sai ta ba shi labari Daga nan ransa ya baci yana mai ccwaga A'isha. "Kul dinki. Lallai Khadija (Allah yaji kanta) ta haifar min da Dahir (Shi ne Abdullahi) da Kasim da Rukayya da Zainab. amma ke kina daga cikin wadanda Allah ya kashc mahaifarsu ba ki haifa min komai ba”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next