Tarihin Fatima Zahra [a.s]



shi ne Allah. Madallah da matattara ita ce alkiyama! Kuma a lokacin ne masu batarwa za su yi hasara. a lokacin da za ku yi nadamar da ba ta amfanar da ku "Ga kowane labari akwai matabbata da sannu za ku san wanda azaba za ta zo masa ta tozartar da shi, kuma za ku san wanda madawwamiyar azaba za ta mamaye shi."

Daga nan sai ta juya wajen Ansar (mutanen Madinah ) ta ci gaba da cewa:"Ya ku taron samari! Ya ku mataimaka addini! Ya ku masu rainon Musulunci! Wane irin rauni ne haka a cikin hakkina? Wace irin gafala ce wannan a kan abin da aka zalunce ni a kansa? Ashe Babana Manzon Allah bai kasance yana cewa "Ana kyaye mutuncin mutum da kiyaye mutuncin yayansa ba? Amma sai kuka farar da wannan a kanmu da sauri. kuka gaggauta aukar da shi a kanmu da hanzari. alhali kuna da dama a kan abin da nake ta kokari a kansa da iko a bisa ga abin da nake ncma. kuma kuna da dama bisa abin da nake nufi. Ko kuna cewa Muhammad ya mutu ne'.' Sai rauninsa ya fadada. barakarsa ta munana. alamannsa ya gurbata. kasa ta yi duhu saboda fakuwarsa. zababbun Allah suka daura fansar kansu daga bauta saboda masifar (fakuwar)sa. rana da wata da taurari suka kisfc saboda masifar (rashin) sa. burace-burace suka yanke. duwatsu suka msuna. aka tozartar da mai alfarma. kuma aka gusar da alfarmar a yayin mutuwarsa. Lallai wallahi wannan balai ne mai girma. kuma masifa ce mai ginna. wadda babu masifar da ta kai kamarta. babu kuma annobar da ta kai sauiinta. Littafin Allah wancla yabonsa ya daukaka-ya sanar da ita a cikinku da yammacinku da safiyarku. ya sanar da sauti mai sauki da kuma mai tsanani a nazar.ce da karance. kuma tnn kafinsa ma abin da ya faru ga Annabawan Allah da Manzanninsa kcnan. hakunci ne na yankc da zartanya ta karshe. "Kuma Muhammad ba wani bane illa Manzo, hakika Manzanni sun gabata kafinsa. Idan ya mutu ko aka kashe shi za ku koma ma abin da kuka baro ne? Wanda ya koma wa abin da ya baro ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma da sannu Allah zai saka ma masu godiya."

Haba 'ya'yan Aus da Khazraj (Bani Qailah) kuna ji kuna gani za a kai mani hari a kan gadon Babana. kuna wurin a kan idanuwanku. kiran yana kai wa gare ku. labarin yana gamowa da ku. kuna masu yawa da tanaji. kunada makami dakartl. kuma a wiirinku ak^yai takobi dagarkuwa.kira na kai maku ba ku amsawa, kururuwa na je maku ba ku kai dauki kuna abin siffantawa da sadaukantaka, aka san ku da alheri da gyara, aka sanku da ku ne zabin da aka zaba da falalar da aka fifita domin mu Ahlul bait. Kun yaki Larabawa, kun jure wahala da gajiya, kuma kun tunkari gwaraza. Ba mu gushewa ballantana ku gushe.Muna umurtar ku kuna umartuwa har lokacin da al'amuran Musulunci suka daidata da mu, alheran ranaku suka yawaita. sautin shirka ya wulakartta, rundunar karya ta natsu, wutacen kafirci suka buce, da'awar shirka ta rushe. har tsarin Musulunci ya kullu. Yaya kuka dimauta bayan bayanin, kuka asirta bayan shelantawa, kuka zamuke bayan gabata. kuka yi shirka bayan imani? Muni ya tabbata ga wasu tnutane! (Ashe ba za ku yaki mutanen) da suka warware rantsuwowinsu ba. suka yi niwa ga fitar da Manzo. sune suka far maku tun a farkon lokaci, shin kuna tsoron su ne? "Allah shi ne mafi cancanta da kuji tsoron sa idan har kun kasance muminai."

Ku saurara! Lallai ina ganin kun riga kun dawwama ga jin dadin ray"uwa. kuka nisanta wanda yake shi ne mafi cancanta ga bayarwa da hanawa tare da wadata. kuka totar da abin da yake a bakinku. kuka amayar da abin da kuka hadiye. "Ku sani idan ku da duk wadanda suke a cikin kasa kuku kafirce, to lallai Allah Mawadaci ne abin yabo"

Ku sani. lallai na fadi abin da na fada ne a kan masaniyata ga tabewar da ta shafe ku. da yaudarar da zakatanku sukc tattare da ita. Na yi wannan (kira gare ku) ne kawai saboda takurar zuciya da kuncin kirji da zogin fushi da kuma gabatar da hujja.

Saboda haka ga ta nan gaba gare ku. sai ku kama ta. tana mai raunannen baya. mai ketaccen dagi. mai w anzajjcn aibi. alamtatta da fiishin Allah da kunyata ta har abada. sadaddiya da wutar Allah wadda ake hurawa, wadda take lekawa a kan zukata. " Abin da duk kuke aikatawa Allah yana gani, "Kuma da sannu nadanda suka yi zalunci za su san wace majuya ce za su juya," kuma ni diyar mai gargadi ce gare ku gaba ga azaba mai tsanani "ku yi aiki mu ma ma 'aikatu ne, ku yijira mu ma masu jira ne. "u

WAFATIN NANA FATIMA (as)!!!

BAITUL - BUKA'I:-

Kamar yadda muka dan yi bayani can baya na yanayi da halin da ta sami kanta na bakin cikin rabuwa da Mahaifinta, ta yadda kullum tana cikin kuka da bakin ciki. ta yadda ba za ta iya kamewa ba, wannan hakika yana faruwa ne saboda abu uku:-

1. Ta fi kowa sanin matsayi da darajar Mahaitinta, muhimmancin rayuwarsa cikin al'umma da abin da wafatinsa ya kunsa na rashi cikin wannan afumma.

2. Abubuwan da za su sami zuriyarta a baya na kisa da dauri a daidai lokacin da kowa ya juya musu baya, ba su da wani mai taimako sai Allah.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next