Tarihin Fatima Zahra [a.s]



a gidan ba ko naje in samo dan uani abin masaaifi na amfani' Sai ta ce 'Ni ina jin kunyar Ubangiju in tambaye ka abin da ban gan ka da shi ba

"Daga nan sai ya tafi neman rance, sai ya samu rancen dmari. Ya juyo don ya yi siyawan kayan abinci. sai ya hadu da Mikdad cikin wani yanayi mai ban tausayi. tsakar rana yana tafe cikin zafin sahara babu takalmi. Sai Aliyu ya tambaye shi yaya ya gan shi cikin wannan halin ko lafiya? Sai ya ce, 'ka bari kawai. abin ba dadin ji". Sai Aliyu ya ce tnasa Ai kuwa ni ba wanda za ka boywa wani abu bane."

"Daga nan 'sai ya ba shi labarin cewa 'Ba wani abu ya fito da ni cikin wannan lokacin ba sai mawuyacin halin da nake ciki da ni da iyalina. Na kasa zama a gado saboda kukan yara. tsawon lokaci ba su sami abin da za su saka a baki ba." Aiiyu na jin haka sai ya fashe da kuka har sai da gemunsa ya jike da hawaye. Sai ya ce masa 'Ni ma abin da ya fito da ni claga gida kenan." Sai ya ce 'Amma ga wannan dinarin da na ranto yanzu ka je ka yi amfani da shi!"

"Daga nan sai ya tafi masallacin Manzo ya yi sallar azahar. la'asar da magnab. Lokacin da Manzo zai fita daga masallaci. sai ya ga Aliyu a sahun farko sai ya kira shi suka fito. Sai ya ce mishi: 'Yau a gidanka zan ci abincin dare. zai samu kodai babu?" Sai Aliyu ya yi shim saboda kunya (domin kuwa Allah ya sanar da Manzo cewa Aliyu ya ranci dinarc. ya je gidansa ya ci abincin dare tare da su).

"Daga nan sai suka nufi gidan Aliyu baki daya. Suna zuwa suka tarar da Fatima tana salla. kusa da ita akwai tukunya a kan murhu tana cin abinci Ta sallama ta fito ta yi wa Mahaifinta barka da zuwa. ya amsa mata ya shafa kanta yana tambayarta lafiyan gida.

"Daga nan sai ya ce mata ta kawo masu abinci. sai ta sauke wannan tukunyar ta debo musu abinci ta kawo gaban shi da Aliyu, Ko da Aliyu ya ga abincin sai mamaki ya kama shi yake cewa: Bai taba ganin mn wannan abinci ba. bai taba jin kamshin abinci inn shi ba Sai ya ce ya Fatima wannan daga ina' Sai Manzo ya ce 'Wannan shi ne sakamakon dinaren da ka bai wa Mikdad!

ZUHUDUN NANA FATIMA (AS)

ZUHUDIJ: Abin da ake nufi da zuhudu. shi ne watsi da tarkacen duniya da juya baya gare su. Ko kuma rashin barin wani abu na duniya ya mallake mutum.'

mutum, sai yadda ya yi da shi, ba sai yadda mutum ya yi da stu oa. Kodayaushe mutum ya kara bege zuwa lahira yakan kara zuhudu ya zuwa ga duniya. A duk lokacin da lahira ta girmama a zuciyar mutum, to duniya takan kara wulakanta a gurinsa, ya daura ganin cewa rayuwar duniya da ababen jin dadinta ba komai suke ba, ba su isa su dauke mishi hankali ko kadan ba.

Misalin shi a nan shi ne kamar yara masu wasa da'yar bebi, ko gargare dss. wanda sau da yawa za ka ga suna fada a kan kayan wasan har sai an raba su. Amma lokacin da hankali ya zo musu sai ka ga duk sun yi watsi da kayan wasan; duk cikinsu babu wanda yake so a gan sfti yana wasa da wannan kayan wasan. don zai sa a raina masa wayo, kuma mutuncinsa yana iya zubewa.

To haka wannan misalin yake ga Waliwan Allah game da wannan duniyar. Suna kallon kyalkyalin duniya a matsayin abin da zai jawo masu kaskanci ne da wulakanci a yyurin Allah. Ba sa neman duniya sukan nemi duniya ne don lahirarsu. Sukan so zama a duniya ne kawai don ibada, sukan nemi kudi ne kawai don infaki (ciyarwa) da biyan bukatun talakawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next