Tarihin Fatima Zahra [a.s]Bayan haka ne sai Nana Khadija ta kira Aminiyarta wacce ake ce mata Nafisa binti Manbalu ta ba ta labarin kaunarta ga Manzo da kuma nufinta nata aure shi in ya yarda. Ta kuma ncmi a Manzo ya sanar da Abi Talib duk abin da ya faru tsakanin shi da Nana Khadija. Sai ya yi muma da jin wannan labarin. Sai ya kira sauran 'yan uwansa kamar Abbas bin Abdul Mutallib da Hamza bin Abdul Mutallib, ya ba su labarin abin da yake akwai. Daga nan suka nufi gidan Waraka bin Naufal don neman izini da "KIDHABA' da kuma daura aure. Ya yin da suka shiga gidan Waraka bin Naufal suka same shi. Bayan sun gaisa. sai Abu Talib ya fara bayani yana tnai cewa: "Godiya ta tabbata ga Ubangijin wannan dakin (Ka'aba). wanda ya sanya mu daga cikin zuriyar Annabi Ibrahim (as) da Annabi Isma'ila (as). ya zaunar da mu Harami Amintacce. ya kuma sanya mu shugabanni. ya sanya albarka cikin garinmu. wanda niuke ciki. Bayan haka wannan Dan Dan’uwanka (Muhammad) ba wani wanda za a gwada shi da shi cikin Kuraishu face ya tserc masa. babu wani wanda za a yi kiyasinsa da shi face ya daukaka a kansa. ba mai adal'cinsa cikin halittu baki daya Duk da shi mai karancin dukiya ne amma dukiya korama ce wacce take kafewa. Ko kuma inuwa ce mai gushewa. Hakika yana neman khadija da aure. Mun zo ne mu nemi izininka. cikin yardanta da umurninta Sannan kuma sadakinta yana kaina zan biya. ko yanzu ko nan gaba. Lalle shi Muhanimadu. na rantse da Ubangijin ka aba babban mutum ne mai madaukakin addini." Ni kuma nake cewa wannan 'KIDHABA din ishara ce ya zuwa Musuluncin Abi Talib domin ita ce musulmi 'yan addini maras karkacewa daga tafarki madaidaici suke yi kafin zuwan Manzo. kuma irinta ake yi bayan zuwan Manzo. kuma irinta ne Manzo ya bar mana a matsayin shari'a har zuwa tashin kiyama. Bayan ya gama sai Warka bin Naufal ya mayar da jawabi bayan godiya ga Allah (swt) yana mai cewa: "Da mu da ku (Banu Abdul- mutallib manyan larabawa ne. babu wani mai jayayya ga matsayinKU cikin Larabawa. kuma babu mai juyar da bukatunku, ko dankwafar da daukakarku ko alfaharinku. Hakika muna kwadayin sada zumunci da ku da igiyar soyayyarku da daukakarku. Ku shaida taron Larabawa ni na aurar da Khadija binti Khuwailid zuwa ga Muhammadu bin Abdullahi a Ga wata ruwayar an ce Abi Talib shi ya biya sadakin. Wata ruwayar kuma an ce ta bar mishi sadakin ba ta amsa ba. Wata ruwayar kuma ita ce bayan da ta yi mishi bayani a Wannan shi ne abin da ya fi inganci game da auren Manzo da Nana khadija (as). Sabanin abin da wasu ke rmyaitoyya wai Mahaitin Nana Khadija (as) ya ki ya aurar mata da Manzo saboda maraya ne kuma talaka ne. Saboda haka sai ta yaudare shi ta ba shi barasa. Da ya bugu ya fita cikin hankalinsa. sai ta sa masa rigar kwalliyaaka buga mandiri. wanda yake nuna cewa aure ya tabbata. Bayan da ya farka daga mayen. sai ya ce mata lafiya ya gan shi haka? Sai ta ce masa "Ai ka aurar da ni ga Muhammad." Sai zai ce bai yarda ba. Sai ta ce ai ko Larabawa za su yi maka dariya a matsayinka na babban mutum ka yi abu ka warware. Sai ya hakura. To wannan ba gaskiya bane. don Mahaifinta ya rasu tun tana karama. kuma aure irin wannan na alfarma ba zai yiwu a yi shi cikin yaudara ba. Ya zo a cikin "Safinatul Bihar" cewa lokacin da aka gama daura auren. Manzo ya tashi zai bi Abi Talib. sai Nana khadija (as) ta ce masa "A"a gidana za mu tafi. Gidana naka ne. kuma ni baiwarka ce." Allahu Akbar!!! Nana Khadija (as) ta gama kw ashe falalar Manzo tun farkonal'amari kowa ya zo daga baya Sudi ya sama sai 'yarta [Fatiama] da mijinta mijinta Imam Aliyu (as) da "yayansu (Imamai). wadanda suka gaje wannan falalar. Wani Sha'ir yana cewa:
|