Tarihin Fatima Zahra [a.s]Rashin lafiyar Manzoya dada tsanani har sai da ya suma. Lokocin da ya farfado sai ya ga Abubakar da Umar da wasunsu a inda yake. Sai ya ce "Ashe ban umurce ku da ku bi rundunar Usama Ibn Zaid ba?" Sai suka kawo uzuri. Amma Manzo ya san abin da ya hana su. Daga nan sai ya ce "Ku kawo min takarda da alkalami zan rubuta muku abin da bayana ba za ku bace ba har abada." Wasu sun mike don umurnin Manzo. Sai Umar ya hana su yana mai cewa kar su kawo, zafin ciwo ne! Bukhari ma ruwaito wannan cikin littafinsa. Wannan ya karama Nana bakin ciki don ta san Mahaifinta bai fadar son rai. duk abin da zai fada wahayi ne. Manzo ya yi nufin yin haka ne don gudun kar abin da ya faru bayansa na sabam ya faru. sannan kuma don hadin kan musulmi na farko da na karshe. Lokacin da ajalinsa ya karato sai Imam Aliyu (as) ya dauki kansa ya daura a kan cinyarsa. daga nan sai ya suma. Nana Fatima (as) ta dube shi ta fashe da kuka ta cewa cikin wake: Mai farin fuska wanda ake shayarwa domin sa Gatan marayxi garkuwari matan da suka rasa miji ko da Manzo ya farfado sai ya ce mata ci.kin raunannen sauti. 'Ya diyata ki ce: "Muhammadu bai zan komai ba sai Manzo, kafm sa Manzanni sun wuce. Idan ya mutu ko an kashe shi za kujuya da baya ne? Duk wanda ya juya da baya bai cutar daAllah da komai ba." Sai ta yi kuka mai yawan gaske. Sai ya yi mata nuni da ta matso gare shi. Sai ya yi mata niagana a kunne. sai aka ga tana danya. Ko da aka tambaye ta. sai ta ce ya ce mata ita ce farkon wanda zai riske shi cikin iyalansa bayan wafatiasa. Bayan wafatinsa da kwana saba'in da biyar ta riske shi.7-9 An aiwaito daga Anas Ibn Malik yana cewa; Fatuna ta zo gurin Manzo sadda bai da lafiya tare da Hasan da Husaini, sai ta rungume sm ta hada kiijinta da nashi tana kuka. Sai Manzo ya ce; "Ya Fatima kada ki yi kuka, kada ki mari fuskarki ko kumatunki irin na jahiliwa har zuwa inda ya fashe da kuka yana cewa: "Ya Ubangijina kai ne mai kula min da iyalan gidana. Ya Ubangijina wadannan sune amanata gare ka da sauran musulmi." An ruwaito daga Imam Musa Ibn Jafar daga Baban sa (as) yana cewa: A dareti da Manzo zai wafati washegarinsa, ya kira Fatima da Aliyu da Hasan da Husaini (as). Sai ya ce a kulle kofa, ba kowa sai su kadai a ciki. Sai ya ce wa Fatima ta matso kusa da shi. Sai ya gana da ita, ganawa mai tsawon gaske. Da Aliyu ya ga haka sai ya fito tare da Hasan da Husaini suka tsaya a bakin kofa. Mutane kuwa sun yi cincirindo a bakin kofar tare da matayen Manzo. Sai A'isha ta ce ya ka fito ka bar Fatima ita kadai cikin wannan lokacin? Sai Aliyu (as) ya ce na san abin da yake gaya mata na daga abubuwan da za su faru bayan wafatinsa." Imam Aliyu yana cewa "Ban jima ba sai Manzo ya aiko a kira ni. Sai na shiga, sai na fashe da kuka. Sai ya ce 'Me ke sa ka kuka ya Aliyu? Wannan ba lokacin kuka bane. lokacin rabmya ne tsakanina da kai. Na bai wa Allah amanarka ya dan’uwanka. Hakika Ubangijina ya zaba min abin da ke gurinsa.' Sai Manzo ya ce 'Ni kukana da bakin cikina da suman da nake yi shine don abin da zai same ka da diyata (Fatima) na wulakanci bayana. Hakika an riga an yi nufin yin hakan. Amma na bai wa Allah amanarku kuma ya amsa. Ni na yi wa Fatima wasiyyoyi in ka tambaye ta za ta fadi maka. Sannan sai ya rungume ta ya sumbanci kanta. Sai ya ce "Mahaifinki fansanki ne ya Fatima. Sai sautinta ya daka sosai saboda kuka. Sannan sai ya kuma rungume ta ya ce: Wallahi sai Allah ya azabtar da duk wanda ya cutar da ke. Allah yana fushi da fushinki. Tsananin azaba ya tabbata ga duk wanda ya zalunce ki' Sannan sai ya fashe da kuka Imam Aliyu ya ce: "Na rantse da Allah sai da na yi zaton wani yanki a jikina ya fita saboda kukan Manzo. Idanuwansa suna zubar da hawaye kamar ruwa, har sai da gemunsa ya jike sharkaf yana rungume da Fatima ba ya so ya rabu da ita!! Ni kuma ina jingine da shi, kansa yana kirjina. Hasan da Husaini suna tsotsan yatsun kafarsa suna kuka!!" Imam Aliyu ya ce. "Da zan ee Mala' ika Jibrilu yana dakin da na yi gaskiya.. Domin ina jin kuka a sasannin dakin. Kuma rta tabbatar kukan Mala'iku ne. Na san bai yiwuwa a wannan daren a ce Mala'ika Jibrilu ba ya tare da Manzo " •
|