Tarihin Fatima Zahra [a.s]NIZARI BN MA'AD: An haife shi ne a shekara ta 64 kafin zuwan Annabi Isa (as). Lokacin da mahaifinsa ya ga hasken fuskarsa (hasken Annabta) sai da ya yanka masa rakuma dubu (1000) saboda murna; sannan ya ciyar da mutanen da ba su da iyaka. Bayan wafatin Mahaifmsa sai ya zama shugaban mutanensa. MADAR (AMRU) IBN NIZAR: Sunan mahaifiyarsa Saudatu. An haife shi ne a shekara ta 31 kafin zuwan Annabi Isa (as). Bayan wafatin mahaifinsa sai wannan hasken ya komo ya zuwa gare shi. sai ya zama shugaban mutanensa. Ya kasance yakan karantar da su addinin kakansa Annabi Ibrahim (as). ILYAS IBN MADAR: An hait'e shi ne a shekara ta biyu kafin zuwan Annabi Isa (as) shi ne ya zama shugaban mutanensa bayan wannan hasken ya komo ya zuwa gare shi. Ya kasance kamar Annabi Lukman wajen sauraron kararrakinsu. matsalolinsu da biyan bukatunsu. har suna masa lakabi da shugaban dangi. Iliyas ya kasance wasu lokuta akan ji sautin tasbihi daga tsatson gadon bayansa MUDRIK IBN ILYAS: Sunan mahaifiyafsa Laila. An haife shi ne a shekara ta 35 bayan zuwan Annabi Isa (as) Ana yi masa lakabi ne da Mudrik. ma'ana wanda yake da kyawawan dabi'un iyayensa. Bayan rasuwar mahaifinsa siii ne ya zama shugaban mutancnsa. KHUZAIMA IBN MUDRIK: Sunan mahaifiyarsa Salma An haife shi ne a shekara ta 68 bayan zuwan Annabi Isa (as) Bayan wafatin mahaifinsa shi ne ya zama shugaban mutanensa. bayan wannan hasken ya koma ya zuwa gare shi. ALNADIR (KURAIS) IBN KINANA: Sunan mahaifiyarsaBarratu. An haife shi ne a shekara ta 134 bayan zinyan Annabi Isa (as). Ana kiransa da suna Nadar ne sabo da kyawun fuskarsa daga rarraba ya zuwa guri guda bayan ya zamo shugabansu. Sukan tartaru kodayaushe a gidansa don cin abinci da sauran biyan bukatu, don haka ne tna ake masa lakabi da Kuraish, ma'ana wanda ake taruwa a gurinsa. Da wannan ne duk kabilar da take jingina kanta ya zuwa gare shi ake kiran ta Kuraishu. MALIK IBN ALNADAR: Sunan mahaifiyarsa Atika. An haife shi ne a shekara ta 167 bayan zuwan Annabi Isa (as). Bayan rasuwar mahaifmsa shi ne ya zama shugaban mutanensa. bayan hasken nan ya koma zuwa gare shi. FIHIRI BN MALIK: Sunan mahaifiyarsa Jundalatu. An haife shi ne a shekara ta 200 bayan zuwan Annabi Isa (as). Bayan rasuwar mahaifinsa shi ne ya zama shugaban mutanensa. bayan wannan hasken ya koma ya zuwa gare shi.
|