Tarihin Fatima Zahra [a.s]



3. Ya yi masa kambi da kambin shiriya

4. Ya sanya tnasa wandon Maarifa

5. Bel dinsoyayya don daure wandon da shi.

6. Ya sa masa takalmin tsoro, ya ba shi sandar girma

Sannan ya ce: Kaje ka kira mutane zmya ga La'ilaha illallah Muhammadur Rasulullah (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. kuma Annabi Muhammadu bawansa ne).

MAHAIFIYAR NANA FATIMA (AS)

Mahaifiyarta itace Nana Khadija (as) binti Khuwailid bin Asad bin Abdul Aziyyu binKusaiyi, daya daga cikin Kakannin Manzo sun hadu da Manzo ta wajen Kakanni. Mahaifiyarta. lta ce Fatima Binti Zaid bin Asan. daya daga cikin kakannin Manzo. Kenan sun hadn ta bangarcn uwa da uba. Suna da tushe mai asali. tushe na gari.

An haife ta ne ga ruyyaya mafi inganci shekara uku kafin shekarar giwaye (568 AD). Tsakanin ta da Manzo slickara uku ne. Haka ya zo a cikin Bihaail Anwar Ya zo a cikin Jannatul Kuld cowa tsakanin ta da Manzo shekara daya ne Ya zo a cikin Sauratul Islam cewa tsakaninta da Manzo shekara takwas ne. Amma abin da ya fi shahara shi ne tsakaninta da Manzo shekara goma sha biyar ne. Nana Khadija (as) ta taso no a babban gida. wanda yake cikc da dangi maabota son adalci. hana zalunci. tarin ilimi da janmta. Ya zo cikin Sira na Ibn Hishani cewa lokacin da rundunar Sarkin Yemen suka shiga Makka don su dauke dutson nan na Hajral Aswad. Usaid bm Abdul Aziyyu. kakan Khadija (as) wanda ta girma a gidansa. yana cikin wadanda suka daura damarar yaki don hana wannan rundunar daukar wannan dutsen Sannan kuma suka hadu a kan ba wanda za a zalunta daga cikin mutanen Makka ko wani wanda ya shigo cikinta face sun tsayu ga hakkinsa har sai an mayar masa da shi ''

Kuma Waraka bin Naufal (Amminta) yana daya daga cikin mutanen nan hudu wadanda suka fara yi wa jahiliyya baraa. suka ki bautar gumaka suka bazama neman addinin gaskiya. Ibn Ishak yana cewa: Wata rana Kuraish sun hadu a idinsu kamar yadda suka saba shekara-shekara Sukan don bauta Sai wasu mutum hudu suka kebe daga cikinsu suna cewa hakika mutanensu sun kauce hanya. "Wadannan duwatsun da ake bauta ma ba su ji, kuma ba su gani. Saboda haka mu rabu da su, mu bazu garuruwa don neman addinin gaskiya na Annabi Ibrahim (as)."

Ko shakka babu Nana Khadija (as) ta taso cikin dangi wanda ba a jayayya wajen asalinsu. da siffantinyarsu da dabru ababen yabawa. Hausawa suna cewa hali zanen dutse. mai shi ba ya rabuwa da shi. Da haka ne ta zama abar koyi ga duk matan da ke ciƙin garin Makka har ma Larabawa suna mata lakabi da Dahira, suna girmamata da ganin kimarta. a daidai lokacin da mata ba su da kinra ko kadan a idon al'umma ta ɗuniya baki daya, ta yadda ko ina kashe su ake yi, ko ma a binne su da ransu tun kafin su girma. Allah (swt) yana cewa: "Idan wacce aka binne da rai ta yi tambaya da wane laifl ne aka kashe ta?" Nana Khadija tana da kima kwarai wajen Larabawa da wadansunsu Ta shahara wajen hulda da Malamai na Attaura da Injila. Daga cikinsu akwai Amminta Waraka bin Naufal. Ta haka ne ta samu kubuta daga bautar gumaka da munanan dabi'u irin na jahiliyya. Sannan kuma wajen mataki babu ya lta. duk cikin matan Larabawa da mazajensu. Y'a zo a cikin tarihi cewa babu wani gida a Makka wanda bai amfana da dukiyarta ba Hasali ma mafi yawa daga cikin magidanta tana bin su bashi bayan mfakin da takc musu Har ma wasu daga cikinsu bayan Manzo ya bayyana sukan yi nufin su je har gida su ci mutuncinsa sai su tuna cewa matarsa tana bin su bashi. sai su kame

Ta kuma shahara wajen sadaka, Saudayawa takan soke rakuma. ta yanka dabbobi. ta rabar sadaka ga mabukata. Sannan kuma ba a bar ta baya ba wajen hidima ga dakin Ka’aba. Ire-iren wadannan ba za su lissafu ba. sai dai mai karatu ya fadada bincike a kai don ya fa idantu sosai Kuma ya gano cewa lallai Nana Fatima (as) ta yi gadon abin arzikj tun farkon duniya har zuwa karshen rayuwarta. Sannan ta bar wannan gadon ga ya yanta da jikokinta har zuwa tashin kiyama. wanda Malam Ibrahim Zakzaky yana daga cikinsu. Ko ba a fada ba abin arziki sai da na kwarai. dana alfarma. wadandaake bai wa tajdidinaddini. Allahya sa mu rabauta. Ammin Nana Khadija (as), kamar yadda muka fada a baya, ta kasance tana hulda da Malamai masana Attaura da Injila. A cikin karantarwar da suke mata ne suka sanar da ita cewa Allah (swt) zai tayar da Manzo a tsakanin Larabawa, wanda shi ne zai zama Annabin karshe. Tun daga wannan lokacin Nana Khadija (as) ta daura tunanin yadda za ta riski wannan Annabin don ta yi imani da shi, ta kuma taimake shi matukar rayuyyarta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next