Tarihin Fatima Zahra [a.s]Bayan haihuwar Zainab da Rukayya sai aka haifi Ummu Khulsum. Mun dan zo da bayaninta a baya wajen bayanin 'ya'yan Abulahabi. Bayan sakin da Utuba ya yi, ta koma gida gurin Manzo.Bayan rasuwar Rukayya, sai Manzo ya aurar da ita ga Usman Ibn Affan. Wannan shi ne dan kadan daga cikin abin da za mu zo da shi, gudun kar littafin ya yi tsawo. Dangane da wannan abin da muka zo da shi game da 'yan uwan haihuwar Nana Fatima (AS) wajen Zainab, Rukayya da Ummu Khulsum, mun zo ne da abm da ya fi shahara cikin littafan tanhi a ruwayoyin mafi yawa daga cikin ruwayoyin Malaman Sunni. Amma abin da ya fi inganci a ruwayoyin Malaman Shi'a da Sunna shi ne su ba 'ya'yan Manzo bane. 'ya'yan 'yar uwar Nana Khadija ne, wacce ake kira da suna Hindu. Sai dai sun girma a hannunsa ne. Ya zo a cikin Albidau wattarikh na Mukaddasi yana cewa: An ruwaito daga Sa'id Ibn Abi Urwatu daga Katada yana cewa: Khadija (AS) ta haifar wa Manzon Allah (SAAW) da Abdulmanaf lokacin . Jahilhya, sannan kuma ta haifar masa da 'yaya maza biyu, mata hudu cikin Musulunci. Alkasim, wanda da shi ne ake masa lakabi da Abulkasim. ya girma zuwa lokacin da ya fara tafiya, sannan ya rasu Sai Abdullahi wanda ya rasu yana karami, sai Ummu Khulsum, Zainab, Rukayya da Fatima (AS) Alkasdalani ya ruwaito cikin Almuwahib, yana cewa: An haifar masa da da wanda ake kira A.bdulmanaf tun kafin saukar wahayi. sai suka zama goma sha biyu. anuna duk cikansu an haife su ne bayan wahayi ya sauka, in banda wannan dan (Abdulmanaf (AS). Abu na biyu kuwa shi ne suratul Tabbatyada an saukar da ita ne a shekara ta biyar bayan wahayi ya sauka. lokacin Manzo da danginsa suna tsare a kogon Abi Talib. Imam Jalaluddin Suyudi ya ruwaito wanari a littafinsa Durrul Mansur. Ita kuwa hijirar farko zuwa Habasha an yi ta ne kafin wannan lokacin. Abin tambaya a nan shi ne yaushe 'ya'yan Abulahabi suka sake su, yaushe ne kuma Manzo SAAW) ya aurar da su ga Usman bin Affan9 Idan mai karatu yana so ya fadada a kan wannan yana iya samun littafin Assahlhu tnin siratin Nabiyil a'azam, da kuma sauran wasu littafan da muka yi amfani da su, in Allah ya so. 'YAN UWAN HAIHUWAR NANA FATIMA (as) MAZA Nana Fatima (as) tana da yan uwa mazagun Mahaifinta su hudu. wadanda
|