Tarihin Fatima Zahra [a.s]



"Sannan ya sadar da igiyarsa da igiyar yyani daga cikin iyalansa, (Imam) Sahabinsa, mai gaskata da'awarsa, mai kuma gaggawa ya zmya ga zancensa, ya aurar da Fatima ga Aliyu." Daga nan sai Malaika Jibrilu ya karasa da fadin AUah na cewa: "Yabo mayafina ne, girma kambuna ne. halittu dukkansu bayina ne. maza da mata. Na aurar da Fatima baiwata ga.Aliyii zababben bawana. ku Mala'iku ku shaida”.

IMAM ALIYU (AS) A MASALLACIN MANZO (SAAW)

Bayan da Manzo ya amshi sulken Imam Aliyu (as) a matsayin sadakin Nana. sai ya ce: "Mu je masallaci ya Aliyu, zan zo in ambace ka cikin jama'a da kyakkyawan ambato, wanda zai faranta maka rai da duk mai kaunar ka duniya da lahira, sannan kuma in daura maka aure da Fatima."

Sai Aliyu ya ce: "Sai na fito daga gidan ina mai farin cikin da ba ya misaltuwa. Sai na hadu da Abubakar da Umar. sai suka tambaye ni yaya aka yi? Sai na ce: Ai Allah (swt) ya daura min aure da Fatima a can sararin samaniya, ga Manzo nan tafe bayana-zai zo ya bayyana ma jama'a. sai suka yi farin ciki sosai da jin haka.

"Sai muka juya zuwa masallaci. Kafin mu zauna cikin mutane Manzo ya iso. fuskarsa cike da farin ciki. Sai ya ce Ina Bilal?" Sai Bilal ya amsa masa. Sai ya ce Ka tattaro tnin Muhajirun da Ansar." Sai Bilal ya fita ya tattaro su duk suka hadu.

"Sannan ya hau mumbari ya yabi Allah. ya yi godiya gare shi sannan ya ce: "Ya ku taron jamaar musulmi. lallai dazun nan Jibnlu ya zo min yana ba ni labari daga Ubangijina Mabimayi da daukaka cewa Ya tara Malaiku a Baitul Maamur ya-shaida masu cewa ya aurar da baiwarsa Fatima ga bawansa Aliyu Ibn Abi Talib. ya kuma umurce ni da in daura mishi a nan doron kasa. don ku zama shaidu.

Sannan ya zauna sai ya ce ma Almi (AS) "Mike ka nema da kanka." Sai ya mikc ya yi godiya ga Allah (swt)-ya yabe shi sannan ya yi salati ga Manzo. Sai ya ce "Dukkan yabo ya tabbata ga Allah a bisa nrimominsa masu yawa, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. shaidawa wacce za ta kai ga samun yardarsa. Allah ya yi dadin tsira ga Annabi Muhammad wacce za ta kara mar kusanci ya zuwa gare shi. Aure yana daga cikin abin da Allah Mabuyyayi da daukaka ya yi umurni da shi. ya kuma yarda da shi.

"Taron nan namu yana daga cikin abin da Allah ya hukunta ya kuma yi izini da shi. Hakika Manzon Allah ya aura min da "yarsa Fatima. ya amshi sulkcna a matsayin sadaki. Amma ku tambaye shi sannan ku yi shaida.

Sai jama'ar musulmi suka Manzo, Manzo ya amsa musu an yi haka Sannan ya yi khuduba da addu'o'i masu kunshe da abubuwa da yawa. Sannan ya koma gidan ya umurci matansa da su buga wa Fatima (AS) mandiri. An daura wannan auren ne ran daya ko shida ga watan Zulhajji cikin shekara ta biyu bayah hijira.7

 

SADAKIN NANA FATIMA (AS)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next