Tarihin Fatima Zahra [a.s] Sayyida zainab (A.S): Sayyida Zainab lta-ce diya ta uku bayan haihuwar Imam Hasan da Husain. An haife ta ne cikin watan Sha aban hijira na,da shekara biyar. Ta taso a hannun mahaifiyarta shugabar matan Aljanna Yayyinta kuma shugabannin samarin gidan aljanna . Ita ma kamar sauran yayiinta Allah ne da kansa ya sanya mata; suna hanun; Mala'ika Jabara'il bayan manzo da Imam sun ce ba zasu shiga gaban Ubangijinsu wajen sanya mata suna ba. Dukkan abubuwan da suka faru bayan rasuwr mahaifiyarta nab akin ciki takurawa da kisa an yi sun e a gabanta tana kallo.Tun daga mahaifinta yake iraklokacin yakin siffin zuwa loakcin da muawiyya ya shira yaki da Immam Hasan(A.S) har uwa uba lokacin da aka kasha imam Husain a karbala. Lokacin da Imam husain (a.S) zai fita yaki da makiya ita ya bauwa amanar Imam Zainul Abidin (a.S) da sayyida sakina a.s tag a bkin ciki da duk iyalan manzo babu wanda ya ga wannan musamman gab da Imama Husain (A,S) zai yi shahada , da bayan ya y shahada munzo da bayaninsa sosai a littafinmu na tarihin Imam Huusain (A.S) bayan karbala ta koma Madina da zama daga nana kuma ta koma Misra saboda matsai daga makiya manzo . A can Allah subhanahu ya yi mata cikawa aka binne ta. 2. sayyida ummu khulsum A.S Bayan haihuwar Zainab sai aka haifi ummu khulsum wacce it ace ta hudu cikin jerin 'ya 'yan Nana Fatima. Ta yi tarayya da sauran 'yan uwanta wajen darajada daukaka da kuma asali. NANA FATIMA A CIKIN AYAR KURBA:Allah (swt) yana cewa: "Ka ce (musu) ba na neman lada a gurinku sai dai nuna kauna ga makusanta.." Wannan ayar kamar yadda ta sauka Allah (swt) yana tnagana da Manzonsa ne a kan ya gaya wa muminai cewa dangane da shiryar da su da ya yi, da tsamar da su daga duhun kafirci zuwa hasken Musuluncu bakar gaba ta jahiliyya zuwa ga soyayya ta Musulunci, bakin talauci zuwa yalwataccen arziki na duniya da lahira, babu wani sakamako da za su yi mishi sai da kawai su nuna kauna da soyayya ga iyalan gidansa. Lokacin da wannan ayar ta sauka sahabbai sun tambayi Manzo a kan su wanene wadannan wadanda Allah ya wajabta mana kaunarsu? Sai Manzo ya ce sune: Aliyu, Fatima, da 'yayansu. A wani hadisin wanda IbnHajri da Dabari (Malaman sunni) suka ruwaito Manzo yana cewa "Allah (swt) ya sanya ya zama sakamakon da za ku yi min a kan abin da na yi maku a nan duniya shi ne ku nuna kauna ga iyalan gidana. Ib Hajri ya ruwaito cewa: Wata rana Imam Hasan yana yi wa jama'a khuduba a masallaci sai yake cewa: ina daga cikin mutanen gidan da Allah(swt) ya wajabta kaunarsu da nnka musu wilaya (shugabanci). A kansu wanene aka saukar da ayar da take cewa 'Ka ce (musit) ha na neman lada a gurinku sai dai nuna kauna ga makusanta..' (ma'ana a kanmu ne wannan ayar ta sauka)" An ruwaito daga Imam Zainul Abidin yana cewa: "Lokacin da aka taho da mu daga Karbala. cikin mari a daurc. an zo za a shiga cikin garin Sham, sai wani mutum ya ce 'Mun gode wa Allah da ya halaka ku_ ya mai da ku haka' Sai Imam Zainu! Abidin ya ce masa "A kanmu ne fa ayar da Allah (swt) yake cewa 'Ka ce (musu) ba na neman lada a gurinku..' ta sauka' Daga nan sai mutumin ya fadi yana kuka. yana neman gafara'"
|