Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Ya zo a cikin Uyunul Akhbar. an ruwaito daga Rawan Ibn

Sult yana cewa: Wata rana an tambayi Imam Aliyu Ibn Musa Ibn Kazim (AS) a Majalisar Ma'amun. ma'anar ayar da Allah (SWT) yake cewa: Arninci ya tabbata ga Ali Yasin. Sai ya amsa da cewa: Babana ya ba ni labari yaji daga babansa. shi kuma ya ji daga babansa Amirul Muminina Aliyu (AS) yana cewa: Yasin shi ne Muhammad (SAAW). mu kuma mune Ali-Yasin.

Sai Malaman da ke kusa kewaye da shi suka ce lallai kam Yasin shi ne Muhammad (SAAW) babu wata shakka. Daga nan sai Imam ya ci gaba da cewa: Lallai kam Allah ya bai wa Muhammad falala mai yawan gaske ta yadda babu wani Annabi wanda Allah ya yi wa iyalansa sallama.  sai iyalan gidan Muhammad (SAAW).

Ya zo a cikin Kitabul Azkar na Imam Yahya Annawawi yana cewa: Tirmizi ya ruwaito daga Abi Huraira yana cewa: Manzon Allah (SAAW) yana cewa: Allah ya wulakanta fuskar duka wanda aka kira sunana a gabansa bai yi min salati ba.

An ruwaito daga Jabin Ibn Abdullah cewa: Manzon Allah (SAAW) yana cewa: Duk wanda aka ambace ni a gabansa bai yi min salati ba, to wannan ya tabe.  An ruwaito daga Aliyu (AS) yana cewa: Manzon Allah (SAAW) ya ce: Marowacin da kawai aka sani shi ne wanda aka ambace ni a gabansa, bai yi min salati ba.

FALALAR SALATI GA MANZO DA IYALAN GIDANSA (AS)

Falalar salati ga Manzo da iyalan gidansa, wannan ba abu ne wanda wani alkalami zai iya rubuta shi ba. ko wani harshe zai iya furuci da shi ba. a nan kawai za mu dan zo ne da wasu daga cikin hadisan Manzo (SAAW) ne, alabashi mai karatu sai ya yi kokari ya fadada ko ta nan Allah zai dube shi da idon rahma.

Ya zo a cikin Kanzul Ummal, Manzo yana cewa: salati a kaina haske ne a kan siradi gobe kiyama.

An ruwaito daga Abdullahi Ibn Nu'uman yana cewa: Wata rana na gaya wa Baban Abdullah (Imam Sadiq) cewa na shiga dakin Ka'aba, amma ban sami komai na addu'a ba sai dai kawai salatin Manzo. Sai ya ce: Lallai babu wani wanda ya fito da abin da ka fito da shi na falala da alheri.

Imam Sadiq (AS) ya ruwaito daga Imani Baqir (AS) yana cewa: Mafi nauyin abin da za a daura a mizani ran kiyama shi ne salatin Manzon Allah (SAAW).

An ruwaito daga Anas Ibn Malik yana cewa: Manzon Allah (SAAW) yana cewa: Duk wanda aka ambace in a gunnsa. to ya yi min salati. domin kuwa wanda ya yi min salati sau daya Allah Mabimayi da Daukaka zai yi masa salati sau goma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next