Hikimar Ziyarar Kaburbura



Idan har Muminai masu sabo sun samu umarni a kan cewa su zo wajenka domin ka nema musu gafara, ni ma ya manzon Allah ya mai ceton al’umma sakamakon halartata zuwa haraminka da sallama zuwa ga kabarinka ina mai yi maka bai’a a kan cewa zan yi kariya ga addininka sannan in yi nesa daga shirka da sabon Allah, sannan sakamakon haka ina rokonka ka nema mini gafara a wurin Allah.

 A nan dole mu fahimci cewa ziyarar kaburburan bayin Allah ya sha bamban da yawon shakatawa domin kuwa yana da manufarsa da ta sha bamban da yawon bude ido. Masu yawon bude ido suna zuwa wuri ne domin su more wa idanunsu, suna neman wurare masu kyau ko na tarihi domin su gane wa idanunsu. Saboda haka gurinsu shi ne: shakatawa da hutawa, duk da cewa idan wannan bai kasance tare da sabon Allah ba, to musulunci ba ya hani da wannan. Amma masu ziyarar kaburburan bayin Allah suna yi ne domin kara samun alaka da masoyinsu da kuma jaddada alkawarinsu da shi, don haka duk wata wahala da zasu hadu da ita wajen isa zuwa gare shi koda kuwa zai kai ga su rika gudu a cikin daji da kafafunsu ne da taka kayoyi suna iya jure wa duk hakan.

 Dan yawon bude ido yana neman abin da zai biya bukatunsa na kasantuwarsa mai rai ne shi, amma mai ziyara yana kokarin ya shayar da ruhinsa ta hanyar saduwa da masoyinsa, domin kuwa ba zai iya isa zuwa ga masoyinsa ba, sai ya mika hannunsa zuwa ga kabarinsa wanda yake dauke da kanshi da launinsa.

 Tarihi yana nuna cewa: Bayan wafatin manzon Allah (S.A.W) wani bakauye ya shigo garin Madina sai ya zauna a gefen kabarin manzo sai ya karanta wannan aya wadda take cewa: “Da wadanda suka zalunci kansu sun zo a gareka suka nemi gafarar Allah Sannan manzo ya nema musu gafara da sun sami Allah mai karbar tuba mai rahamaâ€‌.

 Sai wannan bakauyen balarabe ya ce: Ya kai manzon Allah gani na zo a wannan wuri domin ka nema mini gafara ina mai neman cetonka zuwa ga Allahâ€‌. A lokacin yana cikin kuka sai ya karanta wannan baiti na waka inda yake cewa:

Ya mafificin mutumin da aka bisne jikinsa a wadannan kasashe

Kanshinsa ya bice tudu da kwari na wannan yanki

Ina gabatar da kyautar raina zuwa ga wannan kasa wadda ta boye fiyayyen haliitta[5]

Bayan ya gama wannan baiti na waka sai ya nemi gafara ya tashi ya tafi abinsa.

Wannan balarabe da muka ambata ya fahimci ma’anar ziyarar kabarin manzo daga cikin zuciyarsa tsarkakka, saboda haka ne ya taso ya zo domin ya ziyarci shugaban halitta. Wannan ita ce hikimar ziyartar kaburburan â€کyan’uwa, masoya, malamai, shahidai a tafarkin Allah, da shugabannin addini wanda hankali da shari’a suke tabbatar da ingancinsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next