Hikimar Ziyarar Kaburbura Sannan ya cigaba da cewa girmama Manzo a lokacin da ba shi da rai kamar lokacin da yake da rai ne babu bambanci. Lokacin da Mansur ya ji wannan magana sai ya zo da kansa wajen Malik ya ce: A lokacin da nake addu'a zan kalli kibla ne ko kuwa kabarin Manzo? Sai Malik ya ba shi amsa da cewa: Me ya sa zaka juya wa Manzo baya alhali kuwa shi ne tsaninka kuma tsani ga babanka Adam har zuwa ranar tashin kiyama, don haka ka kalli kabarin Manzo ka nemi ceto daga gare shi Allah ya amshi cetonka. Allah yana cewa: A lokacin da suka zalunci kawunansu suka zo gare ka suna neman gafarar Allah manzon zai nema musu gafara..."[47] Ziyarar Kabari Da Kiyaye Asali A cikin wannan bahasi namu mai tsawo kawai mun yi amfani ne da ruwayoyin da suke nuni a A nan zamu kara da cewa, kiyaye abubuwan da suke na asali yana daya daga cikin ayyukan addinin musulunci. Abin da muke nufi da asali kuwa shi ne abin da yake bayyanar da gaskiyar musulunci da cigabansa har ya isa zuwa ga dukkan zamuna. Addinin musulunci addini ne da yake na duniya baki daya, don haka har zuwa tashin kiyama zai kasance matsayin addini cikakke har karshen duniya. Saboda haka dole ne mu yi iya kokarinmu mu ga cewa mun kiyaye asalin wannan addini don ya isa kamar yadda ya zo zuwa ga wadanda zasu zo a nan gaba. Saboda haka ziyarar kabarin Manzo da Ahlul Bait (A.S) yana daya daga cikin kiyaye asalin addini, don haka barin hakan bayan wani tsawon zamani sai ya zamana an manta da wannan babban aiki mai albarka. Saboda haka dangane da wadanda zasu zo nan gaba sai ya zamana wadannan wurare na musamman na manyan bayin Allah ya koma kamar wani abin tatsuniya. Kasancewar zuwan Isa (A.S) a yau wani abu ne wanda ba abin shakka ba ga al'ummar musulmi, amma a yammacin duniya musamman ga matasa al'amarin Annabi Isa ya zama kamar wani abin tatsuniya, wannan kuwa ya faru ne sakamakon rashin wani abu wanda yake nuna gaskiyar samuwar shi Annabi Isa (A.S) a hannayen mutane. Wannan kuwa ya faru ne sakamakaon canza littafinsa da a ka yi, don haka dangane da shi kansa Masih da mahaifiyarsa da sauran manyan sahabbansa babu wani abu na hakika wanda yake tabbas daga garesu yake. Don haka sakamakon tsawon zamani a yau al'marin masihiyya ya zamana kimarsa ta rage kuma ya shiga cikin wani halin kokwanto da rashin tabbas. Kamar yadda a yau ziyarar Manzo wadda take daya daga cikin abu na asali a cikin addinin musulunci kuma mai nuna hakikanin matsayi da samuwar Manzo tana neman ta zama wani abu marar muhimmanci a cikin al'ummar musulmi, kuma ya zamana an ajiye ta a gefe guda. Don haka sakamakon tsawon zamani akwai yiwuwar abubuwan asali na addinin musulunci da waliyyan Allah, su shiga cikin wannan hadari mai girma. Saboda haka al'ummar musulmi dole ne su tashi tsaye domin kare wannan hadari da ya fuskanto su, wannan kuwa yana samuwa ne ta hanyar kiyaye duk wani abu da ya shafi sakon manzanci da Imamanci, ta yadda za a rika tuna shi a kowane zamani. Saboda haka ziyarar wadannan manyan bayin Allah tana daya daga cikin hanyoyin kiyaye su daga bacewa da kuma yin tunani a kansu a kowane lokaci. Saboda haka sakamakon yin hakan ba za a taba watsi da matsayin wannan muhimmin al'amari ba, ta yadda za iya kulle kofar ganawa ta hanyar ruhi da wadannan manyan bayin Allah ga al'ummar musulmi.
|