Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Mu dauka cewa mahaifiyar mumini sai ta rasa danta aka kuma rufe shi a karkashin kasa, sai ta damu a kan hakan, abin da kawai zata iya yi a nan shi ne ta ziyarci kabarinsa. A nan idan aka hana ta yin wannan aiki wanda ya dace da hankali kuma dukkan mutanen duniya sun tafi a kan hakan, wannan zai haifar da muguwar damuwa ga zuciyar uwa. Shin musulunci zai yi hani da irin wannan aiki sannan kuma ya zama addini mai sauki?

 Kai asali ma ziyarar kaburbura wani darasi ne kuma mai sanya mutum ya rika tunawa da lahira wanda kuma ya kunshi karanta wa wadanda aka ziyarta fatiha. Ta yaya za a hana mata dangane da samun wannan falala?

 Da wani kalamin kasantuwar hikimar ziyarar kaburbura tana kunshe da daukar darasi da tunawa da lahira, ta yaya za a kebance maza kawai ban da mata a ciki?

 Kasantuwar ziyarar kaburbura ya nisanta da duk wani sabo, idan muka dauka haka kuma sai aka hana mata a wancan lokaci, to kila sakamakon cewa ba su kiyaye sharuddan da suka kamata ne.

Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma A Mahangar Malaman Hadisi Da Fikihu

Tare da bibiyar maganganun manyan malaman hadisi da malaman fikihu, zamu ga yadda kodayauhse malaman musulunci suke karfafawa a kan kasantuwar ziyarar kabarin manzo a matsayin mustahbbi mai karfi, Sannan suna kiran mutane zuwa ga ziyarar kabarin manzo mai tsarki.

 Takiyyuddin Subki Shafi’i (ya rasu shekara ta 756) Wanda yake daya daga cikin manyan malaman karni na takwas. Yayin da yake kalu balantar akidun Ibn Taimiyya wanda yake inkarin ziyarar kabarin manzo (S.A.W), ya rubuta littafi mai suna (shifa’us sikam fi ziyarati khairil anam) a cikin wannan littafi ya yi kokari ya tattaro ra’ayoyin malaman Ahlus Sunna tun daga karni na hudu har ya zuwa lokacinsa a kan wannan al’amari, a cikin wannan littafi nasa ya yi kokarin tabbatar da nuna cewa ziyarar kabarin manzo yana daga cikin abubuwan da aka sallama a cikin fikihu a kan cewa mustahabbi ne. Manyan malaman hadisi da fikhu sun ruwaito hadisai daban-daban a kan kasantuwar ziyar manzo a matsayin mustahabbi, sannan suka ba da fatawa a kan hakan.[19]

 Allama Amini wanda yake bincike na wannan zamani kuma mai tsanantawa wajen bincikensa (1320-1390), a cikin babban littafin nan nasa “Algadirâ€‌ Ya yi kokari wajen cike abin da ya ragu a kan wannan batu na ziyar kabarin manzo, inda ya yi kokari ya zo da ra'ayoyin malamai arbai’n wadanda suka hada da malaman hadisi da na fikhu har ya zuwa malaman zamaninsa. [20]

 Wannan marubuci shi ma ya yi kokari ya samo wasu daga fatwoyin da ba su zo ba a cikin wadancan littattafan guda biyu da muka ambata. Ta yadda ya kawo su a cikin wani karamin littafi da ya rubuta a cikin harshen larabci.

 Kai har da babban mai fatawar Kasar Sa’udiyya wato sheikh Abdul Aziz bn Baz ya ba da fatwa a kan mustahabancin ziyarar kabarin manzo mai girma.[21]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next