Hikimar Ziyarar KaburburaWadannan kalmomin sune suka zo a cikin wannan hadisi; Dangane kalma ta farko zamu yi bayani ne a Ya zo a cikin Tajul Arus cewa: Sharaf ma’anarsa shi ne wani wuri mai tudu, wato madaukaki. Sannan ana kiran tozon rakumi da sharaf, Sannan wurare masu bisa kamar gidajen sarakuna ana kiransu da Sharaf, Haka nan akan kira tudun da yake a Tare da kula da ma’anar Dangane da kalma ta biyu kuwa muna iya bayani kamar haka: Kalma ta Sawwaitahu da ta zo da ma’anar aiki wato baje wani abu ko dai-daita shi, ana mafani da ita a cikin harshen larabci da ma’anoni guda biyu. 1-Daidaita wani abu da wani abu daban ta hanyar tsawo ko girma ko makamancin haka. Saboda haka idan da wannan ma’ana 2-Ma’ana ta biyu kuwa shi ne baje wani abu ta yadda zai daidaita babu tudu da kwari, saboda haka a nan wannan fi’ili na sawwa yana bukatar maf’uli guda daya, ba shi bukatar na biyu. Saboda haka duk lokacin kafinta ya daidaita wani katako, kawai zai ce na goge katako, (wato sawwaitul khashab). [89] Saboda haka bambanci wannan ma’anoni guda biyu a bayyane yake, wato a ma’ana ta farko siffa ce ta abubuwa guda biyu, amma a ma’ana ta biyu kuwa siffa ce ta abu guda (wato daidaita wani abu ba tare da an hada shi da waninsa ba kamar yadda muka gani). Saboda haka yanzu mun fahimci ma’anonin wadannan kalmomi guda biyu: wato "Sawwaitahu da musharrafan". Saboda haka muna iya fahimtar cewa wannan hadisi yana magana ne dangane da yadda wannan kabari yake domin kuwa yana magana ne a kan abu guda, ba wai kabari ba da kasa (wato ba a daidaita shi da kasa ba wato a daidaita shi kansa kabarin) Domin da haka ake nufi sai a ce "sawwaitahu bil ard". Saboda haka abin da Imam yake nufi a cikin wannan hadisi shi ne, duk inda ya ga wani kabari yana da tudu da kwari kamar tozon rakumi ya dai-daita shi ya gyara shi ya zama kamar dakali. Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana yadda za a yi kabarin musulmi ta yadda za a baje samansa ba a yi masa tulluwa ba kamar bayan rakumi ko kifi.
|