Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Tafiye-tafiye domin bude ido zuwa wuraren da aka rufe annabawa da â€کya’yansu wani abu ne wanda yake ba sabo ba a cikin al’umma. Wannan kuwa yana nuna cewa mabiya annabawa suna nuna kulawa ta musamman dangane da wadannan wurare, tare da gina gine-gine a kan kaburburansu suna kare su daga rushewa. A yanzu a kasashen Iraki, Palasdin, Jordan, Misra da Iran, akwai kaburburan annabawa (A.S) wadannan aka yi gine-gine masu kawatarwa ta yadda kodayaushe mutane suna zuwa wurin domin ziyara. Sannan dakarun musulunci da su kai hare-hare don bude garuruwan Sham, sam ba ruwansu da wadannan kabuburan annabawa, ba ma haka ba kawai sun bar mutanen da suke hidima a wadannan wurare don su cigaba da aikinsu a wajen kamar yadda suke a da. Sannan ba su nuna rashin amincewarsu a kan hakan ba ko kankani. Idan da yin gine-gine a kan kaburburan annabawa wani aiki ne da ya haramta kuma ya shafi shirka, da wadannan dakaru da suka zo da umarnin khalifa domin bude wadannan garuruwa duka sun rusa wadannan gine-gine, amma koda wani dan karamin canji ba su yi ba ga wadannan kaburbura an cigaba da tafiyar da su kamar yadda suke kafin wannan lokaci. Sannan har zuwa yanzu wadannan gine-gine suna nan kamar yadda suke ta suke jawo hankalin al’ummar musulmi da ma duk mai bin addinan da Allah ya aiko da su.

 Sannan a farkon zuwan musulunci ma musulmai sun rufe annabinsu a cikin dakinsa, kuma babu wani daga cikin wadannan musulmai da yake tunani cewa yin gini a kan kabarin Manzo haramun ne.

 Sannan binciken littattafan tarihi da labaran tafiye-tafiyen masana addinin muslunci yana bayar da shedar cewa akwai daruruwan kaburbura a kasar da wahayi ya sauka da sauran kasashen musulmi:

1-Mas’udi wanda ya rasu 345Bh. wanda yake shahararren masanin tarihi ne, ga abin da yake cewa dangane da kaburburan imamai (A.S) da suke a "bakiyya" yana cewa:

"A bisa kaburburansu a akwai dutse wanda aka rubuta: Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah wanda yake kashe al’umma yake kuma raya matattu. wannan shi ne kabarin Fadima "yar manzon Allah (S.A.W) wadda take ita ce shugabar matan duniya. Da kabarin Hasan bn Ali bn Abi Dalib da kabarin Ali bn Husain bn Ali bn Abi Dalib da kabarin Muhammad Bn Ali Bn Husain bn Ali Bn Abi Dalib da Kabarin Ja’farus Sadik Bn Muhammad". [74]

 Mas’udi ya kasance daga cikin masana tarihi na karni hudu Bayan hjira. ’Yan salafiya wadanda suke da kankamo sun tafi a kan cewa, wannan karni da karnonin da suke kafinsu su ne fiyayyun karnonin tarihin musulunci, sannan ayyukan da suka yadu a tsakanin musulmi a wannan zamani suna nuna kasantuwar abubuwan da shari’a ta yarda da su. Amma abin bakin ciki wannan babban dutse wanda Mas’udi yake fada wanda aka yi wannan rubutu a kansa, sakamakon rushewar da wahabiyawa suka yi wa "bakiyya" yanzu babu shi a samuwa. Saboda haka yanzu wadannan kaburbura ba a iya bambance su.

 Ibn jubair[75] (540-614) shahararren mai yawo bude ido ya ziyarci kaburburan annabawa da bayin Allah a kasashen Misra, Makka, Madina, Iraki da Sham, yayin tafiye-tafiyensa kuma ya yi bayani a kan kowane daya daga cikinsu a cikin littafinsa na tafiye-tafiye, ta yadda dukkammu zamu iya samun wannan a cikin wannan littafin nasa. Ta hanyar karanta wannan littafin musulmi suna samun masaniya a kan tarihin gina hasumiyoyi da gine-ginen kaburburan annabawa da waliyyan Allah. Dangane da abin da ya zo a cikin wannan littafin tafiye-tafiye nasa shi ne: Tarihin gina manya-manyan gine-gine a kan kaburburan Imamai da waliyyai da shahidai a tafarkin Allah, wanda yake komawa zuwa ga zamanin sahabbai da tabi’ai. Wanda yake nuna yadda a wancan zamanin da musulmai suke nuna kauna da kulawarsu dangane da shugabanni da manyan addini, ta yadda suka tashi domin gina wurare masu kawatarwa domin girmamawa gare su. Sannan babu wani daga cikin sahabbai wanda ya nuna cewa wannan aiki yana komawa ne zuwa ga shirka ko kuma ya saba wa tauhidi da kadaita ubangiji.

 Kamar yadda Ibn Jubair ya fara tafiyarsa daga gaban duniyar musulunci (Andulus) zuwa yammacinta ta yadda kasar Misra ta kasance wuri mafi kusa gare shi, Sai ya fara da wuraren tarihin da suke a Misra musamman Alkahira. Zamu kawo wasu daga cikin abin da ya rubuta daga cikin wadannan gine-gine na musulunci a wannan kasa:

Gini Mai Girma Na Kan Imam Husain A.S A Alkahira

 Wasu sun tafi a kan cewa an rufe kan Imam Husain (A.S) a garin Alkahira, saboda haka suka gina wani wuri da sunan "Ra’asul Husain" inda mutane suke zuwa ziyara daga cikin gida da waje. Masu sabon aure a wannan gari sukan je Masallacin Husain (A.S) wanda yake a wannan wuri sukan yi dawafi.. [76]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next