Hikimar Ziyarar Kaburbura |
Next |
Amsar wasu tambayoyi guda biyu
Wasu sun haramta ziyarar mata zuwa kaburbura, suna kafa hujjarsu ne kuwa da wadannan hadisai guda biyu kamar haka:
1-“Allah ya la’anci mata masu ziyarar kabariâ€‌.
Amsa:
Wannan Hadisi ya rasa sharuddan da ya kamata ya kasance yana da su kafin a iya kafa hujja da shi. Domin bisa ga dogara da dalilai da aka ambata a baya dole ne mu dauka wannan hadisi an shafe shi, Sannan cikin sa’a wasu daga cikin malaman hadisi na Sunna sun dauki wannan hadisi matsayin shafaffe. Tirmiz maruwaicin wannan hadisi yana cewa: Wannan hadisi an shafe shi domin yana nuna lokacin kafin halasta ziyartar kabari ne, amma lokacin da manzo ya halasta ziyarar kaburbura wannan hukunci ya hade mace da namiji babu bambanci.
Kurdabi yana cewa: Wannan hadisi yana Magana ne a
2-Ibn maja yana ruwaito daga Ali bn Abi Dalib cewa: Manzo (S.A.W). Ya fito sai ya ga wasu mata a zaune, sai ya tambaue su me ya sa suke zaune? sai suka ce: Muna jiran jana’iza ne.
Sai ya ce zaku yi wa jana’izar wanka ne?
Suka ce: A’a.
back | 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 | next |