Hikimar Ziyarar Kaburbura Saboda haka kiran da a aka yi a cikin dukkan wadannan hadisai guda biyu da cewa "ku ziyarci kaburburaâ€‌ duk da cewa ya fuskantar maza ne amma sakamakon haka ya hada maza da mata ne. Bayan wannan hadisi kuma a kawai wasu ruwayoyi da suke nuni da halascin ziyarar kabari ga mace, saboda haka a nan zamu ambaci wadannann hadisai kamar haka: 1-Muslim yana ruwatowa a cikin sahih dinsa daga manzo cewa: Jibril ya sauko zuwa gare ni ya ce da ni: Ubangijinka yana ba da umarni da a ziyarci kaburburan mutanen “Bakiyyaâ€‌ Sannan ka nema musu gafara a wajen Allahâ€‌. Sai manzo ya tashi daga bisa shimfidarsa ya tafi Bakiyya domin ziyara, sai A’isha ta bi manzo (S.A.W) daga baya, sai ta fahimci umarnin da Allah ya aiko wa manzo. A lokacin sai ta tambayi manzo cewa: to yaya zan ziyarci mutanen baki? Sai manzo ya ce: “Ki ce amincin Allah ya tabbata ga nutanen wannan gida daga musulmai da muminai, Allah ya gafarta wa wadanda suka Wurin da ake kafa dalili a nan shi ne wajen koyar da A’isha yadda ake ziyara, saboda haka idan ya zamana bai halitta ba mace ta ziyarci makabarta, a nan babu ma’ana manzo ya koyar da matarsa. Sannan bugu da kari A’isha ta kasance tana 2-Fadima (A.S) â€کyar manzo (S.A.W), kuma daya daga cikin mutanen mayafi (wadanda aka saukar da aya ta 33 suratul ahzab a kansu) Bayan wafatin manzo ta kasance tana ziyartar kabarin amminta wato shahidin Uhud inda take yin salla raka’a biyu sannan ta yi kuka a kabarinsa. Hakim Nishaburi bayan ya ruwaito wannan ruwaya yana cewa: wadanda suka ruwaito wannan ruwaya dukkansu amintattu ne kuma adalai, ta wannan fuskar ba su da bambanci da maruwaitan Bukahri da Muslim[15]. 3-Tirmizi ya ruwaito daga Abdullahi Bn Abi Malika yana cewa: Lokacin da Abdurrahman bn Abibakar ya rasu a wani wuri da ake kira da (Hubsha) Sai aka dauki jana’izarsa zuwa Makka aka rufe shi a can. Bayan wani lokaci sai A'isha wadda take â€کyar uwa ce a gare shi ta zo Makka domin ziyarar kabarin Abdurrahaman dan’uwanta, Sannan ta yi wasu wakoki guda biyu wadanda suke nuna tsananin damuwarta a
|