Hikimar Ziyarar KaburburaMatsayin Gidajen Annabawa A Cikin Kur’ani Gidajen annabawa da manyan bayin Allah suna da wani matsayi na musamman, wannan kuwa a fili yake matsayin da suke da shi bai shafi wani abu na duniya ba ne, domin idan da haka ne, gidajensu ba su da wani bambanci da sauran gidajen mutane domin an gina su ne da yumbu da tubali kamar na kowa. Wadannan gidaje suna da wannan matsayi ne sakamakon mutane masu matsayi da suka zauna a cikinsu. Kur’ani mai girma[57] yana siffanta hasken ubangiji da fitila mai haske ta yadda yake haske kamar tauraruwa. A ayar da take biye ma wannan aya kuwa ya nuna cewa wurin wannan haske yana gidajen wasu mutane masu girma wadanda suke ambaton Allah a ciki safiya da yamma.[58] A cikin wannan aya jimlar da take cewa "Ana tasbihinsa safiya da yamma, tana nuna dalilin da ya sa aka daukaka wadannan gidajen wadanda aka ambata a cikin ayar da ta gabata. A ayar da take biye mata kuwa an siffanta masu yin ibada a cikin wadannan gidaje ne, inda yake cewa: "mutane ne wadanda kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da salla, domin suna jin tsoron ranar da zukata da idanu suke jujjuyawa suna tsorata.[59] Wannan aya tana bayani ne a 1-Me ake nufi da gidaje a cikin wannan aya? Masu tafsiri sun yi sabani a A-Ana nufin gidaje a cikin wannan aya da masallatai guda hudu B-Ana nufin dukkan masallatai ne a cikin wannan aya C-Ana nufin gidajen Manzo ne
|