Hikimar Ziyarar Kaburbura Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan, saboda haka kawai a nan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu. Wadanda suke son karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama. Hadisi na farko: "Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a gareshi"[41]. wannan hadisi Allama Amini ya ruwaito shi tare da sanadi daga littafi 41. Hadisi na biyu: Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir, Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi bn umar, Manzo yana cewa: "Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo, to ya wajaba in cece shi a ranar kiyama. " Hadisi na uku: Darul Kutni ya ruwaito daga Abdullahi bn umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina a lokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. " Hadisi na hudu: Darul kutni ya ruwaito daga bn Umar cewa manzo (S.A.W) ya ce: "Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. " A nan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Imaman Ahlul-bait (A.S) Ziyar Manzo A Ruwayar Ahlul-Bait (A.S) 1-Imam Bakir (A.S) yana cewa Manzo (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni ina raye ko bayan na yi wafati zan kasance mai cetonsa a ranar kiyama"[42] 2-Imam Ali (A.S) yana cewa: "Ku cika hajjinku da manzon Allah a lokacin da kuka fito daga dakin Allah, domin kin ziyartarsa rashin girmamawa ne gare shi, an umurce ku da yin hakan, tare da ziyarar kaburburan da aka umurce ku zaku karashe hajjinku." 3-Imam Sadik (A.S) daga manzon tsira (S.A.W) yana cewa: "Duk wanda ya zo Makka don aikin hajji amma bai ziyarce ni ba, zan banzatar da shi a ranar tashin kiyama, wanda kuwa ya ziyarce ni cetona ya wajaba a garesa, duk wanda cetona ya wajaba a garesa, aljanna ta wajaba a garesa. Saduk: Ilalish shara'i'i
|