Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Muhammad bn Mahmud wanda aka fi sani da Ibn Najjar wanda yake shi ma shahararren musulmi mai yawon shakatawa ne a cikin littafinsa "Madinatur Rasul" yana cewa:

 "Akwai wata dadaddiyar hasumiya mai tsawo a farkon makabartar "bakiyya" wadda take da kofofi guda biyu wanda kowace rana ake bude daya daga cikinsu domin masu ziyara.[79]

 Wadannan suna daga cikin littattafan tafiye-tafiye da muka dauko daga cikinsu, sannan ana iya komawa zuwa ga wasu littattafai na tafiye-tafiye wadanda suke tabbatar da yin gine-gine a kaburburan annabawa da bayin Allah wani abu ne da yake sananne kuma wata Sunna ce mai tsawon tarihi a tsakanin masu kadaita Ubangiji.

 Ibn Hajjaj bagdadi (262-392) wanda yake mawaki ne shararre a iraki ya yi wata kasida ta yabon Imam Ali (A.S), sannan ya yi wannan kasida ne a haramin Imam Ali (A.S) a cikin taron mutane, a farkon wannan kasida ga abin yake cewa: "Ya kai ma’abocin wannan hasumiya fara a garin Najaf duk wanda ya ziyarce ka kuma ya nemi ceton Allah daga gareka to Allah zai karbi cetonsa". Wannan baiti yana nuna cewa kabarin Imam Ali (A.S) a farkon karni na hudu ya kasance yana da hasumiya.

Abin mamaki a nan shi ne a mahangar ilimin Usulul fikh haduwar mutane a kan hukuncin wani abu har zuwa karnoni da dama yana nuna ingancin wannan abin ne. Amma musulmi sun hadu a kan ingancin gine-gine a kan kabarin annabawa da waliyyan Allah tsawon karnoni masu yawa, amma mahangar wasu wannan bai isa ya zama dalili ba, ta yadda kowane lokaci suna kokarin kaucewa a kan yarda da wannan al’amari.

Gine-Ginen Tunawa Da Bayin Allah Da Dalilai Masu Sabani A Kan Haka

 Mun yi bincike a kan dalilan da suke nuni da ingancin ziyar da girmama kaburburan bayin Allah daga Kur’ani da Sunna da tarihin magabata, amma yanzu lokaci ya yi da zamu yi bincike a kan dalilan masu inkarin hakan. Wanda sukan yi riko da hadisin Abil Hayyaj Asadi ne a kan hakan, yanzu zamu auna wannan hadisi ta yadda zamu ga kimarsa ta hanyar ma’aunin da ake gane ingancin hadisi.

 Muslim a cikin sahih dinsa yana ruwaitowa daga Abil Hayyaj kamar haka: "Ali bin Abi Dalib ya ce da ni: Ba na aike ba a kan abin da Manzo ya aika ni a kansa ba, kada ka bar wani hoto sai ka lalata shi, ko wani kabari mai tudu sai ka daidaita (baje) shi."

 Masu adawa da wannan al’amari suna kafa dalili ne da wannan hadisin a kan haramcin gina haramin wani Imami daga cikin Imamai (A.S) sakamakon haka ne a shekara ta 1344Bh suka rusa makabartar "bakiyya" a wannan rana ne kuma a cikin jaridar "Ummul kura aka sanya tambaya da amsa dangane da dalilan da suka sanya aka rusa wannan makabarta, domin mu gane ta yadda aka kafa hujja da wannan hadisi yana da kyau mu yi bincike a kan ma’ana da kuma dangane wannan hadisi:

A-Sanadin Wannan Hadisi



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next