Hikimar Ziyarar KaburburaD-Masallatai da gidajen Manzo A cikinwadannan ma’anoni da aka ambata a kasa ma’ana ta uku ce kawai zata iya dai-dai kamar yadda zamu kawo dalilai da suke karfafa hakan. 1-Ta fuskar lugga Saboda haka fassara Da wani kalamin ma Bait ya samu asali ne daga baituta wato mutum ya tsaya wani wuri har zuwa safe. Idan har ana mabata gidan mutum da bait saboda mutum yana kwana a cikin wannan gida ne har zuwa safe. Tare da kula da wannan ma’ana ta kalamar bait, fassara ta da ma’anar masallaci yana bukatar abin da yake nuna hakan, ba tare da wannan ba ba za a karbi wannan fassara ba. 2-Kur’ani duk lokacin da zai yi magana a kan wurin da al’umma suke bauta yana amfani ne da kalmar "masjid" ko "Masajid" ne. Sakamakon haka ne wannan kalma an yi amfani da ita sau 28 acikin Kur’ani mai girma. Amma duk lokacin da za a yi nagana a Idan Kur’ani ya kira masallacin Ka’aba da "baitullahi"[60] ba don yana wurin bautar Allah ba ne, domin kuwa mun san cewa Ka’aba alkibla ce ta masu bautar Allah ba wurin da ake ibada ba. Saboda haka hada sunan Allah da wannan wurin kawai yana nuna girmamawa ne, kai ka ce wannan gida na Allah ta yadda za a girmama shi girmamawa ta musamman. 3-Akwai muhimmin bambanci tsakanin masallaci da gida, Bait ana nufin bangaye guda hudu da aka yi wa rufi, amma masjid kawai bangaye guda hudu ne, wato rufi ba sharadi ba ne kafin ya zama masallaci. Da yawan akan gina masallatai a wuraren da suke da zafi ba tare da rufi ba, wanda daya daga cikinsu shi ne masallacin ka’aba, alhalin kuwa gidan da mutum yake kwana yana bukatar rufi. Wannan aya da zata zo a kasa tana bayar da sheda a
|