Hikimar Ziyarar Kaburbura



A nan dole ne mu yi bincike ta mahanga daban-daban a kan ziyarar kabari kamar haka:

1-Ziyarar kabarin muminai a mahangar Kur’ani da Sunna

2-Mata da ziyarar kabari

3-Ziyarar kabarin manzo a mahangar manyan malaman musulunci

4-Ziyarar kabarin manzo a mahangar Kur’ani da Sunna

A nan gaba zamu yi bahasi ne a kan wadannan abubuwa guda hudu da muka ambata a sama:

Ziyarar Kabarin Muminai A Mahangar Kur’ani Da Sunna

 Ziyarar kabarin muminai musamman wadanda suke da alaka ta jini da mutum, wani abu ne wanda duk mutanen duniya sun hadu akan yin hakan domin kuwa ya dace da halitta mutum, sannan muna iya fahimtar haka daga wannan aya: “Kada ka sallaci kabarin wanda ya mutu daga cikinsu har abada, Sannan kada ka tsaya a kan kabarinsa domin kuwa lallai sun kafirce wa Allah da manzonsa, Sannan sun mutu alhalin suna fasikaiâ€‌. [6]

 Wannan aya mai girama tana ba wa manzo umarnin abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Kada ya yi salla ga wadanda suka mutu daga cikinsu da cewa: Har abada kada ka sallaci daya daga cikinsu idan ya mutu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next