Hikimar Ziyarar Kaburbura



A- Nuna farin cikin yayin da masoyi yake cikin farin ciki, da nuna bakin ciki yayin da masoyi yake cikin bakin ciki;

B-Gabatar da buki na farin cikin a lokacin haiwuwar Manzo ko lokacin tayar da shi a matsayin ma’aiki;

C-Yada maganganunsa da abin da ya rubuta;

D-Kiyaye kayan tarihin da suka shafe shi;

D-Girmama Kabarinsa da yin gini domin kiyaye shi daga lalacewa;

Aikata wadannan abubuwa da makamantansu wadanda suke sun halasta a musulunci, yin su ga Manzo da iyalan gidansa ya nuna kauna ne a gare su.

Tirmizi yana ruwaitowa a cikin sunan dinsa: "Manzo (S.A.W) ya kama hannun Hasan da Husain sai ya ce: Duk wanda yake so na ya kuma so wadannan yara guda biyu da babansu da mamansu, to zai kasance a matsayina a ranar kiyama[73].

 Kowannenmu ya san da cewa babban jikan Manzo yana rufe ne a "bakiyya" Sannan mai biye masa yana rufe a Karbala, Sannan wadannan wurare kodayaushe suna ganin al’ummar musulmi masu ziyara, Saboda haka duk wani gini kowane abu wanda za a yi domin kiyaye wadannan wurare, nau’i ne na nuna soyayya ga wadannan jikoki na Manzo kuma bin umarnin Manzo ne a kan soyayya gare su, kamar yadda muka yi bayani a ruwayar da ta gabata.

 A yau al’ummu da dama suna kokari wajen tunawa da manyan tarihinsu (kamar sojoji da â€کyan siyasa da wadanda suka yi wasu ayyuka na gyara) ta hanyoyi daban-daban, sakamakon haka ne suke halarta jana’izarsu yadda ya kamata. Sannan su rufe a wani wuri na musamman a karkashin gini mai kawatarwa, ta yadda wadanda zasu zo a nan gaba kamar yadda na yanzu suke kulawa ta musamman a kan su, suma su yi kulawa da girmamamawa ta musamman a kan wadannan manyan mutane. Don haka mu ma musulmi dole mu yi kokari don yin gine-gine da zasu kare kabuburan manyan mutanemmu.

Kaburburan Manzanni Da Tarihin Magabata Ma’abota Taihidi



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next