Hikimar Ziyarar KaburburaMaruwaitan wannan hadisi su ne kamar haka: 1-Waki 2-Sufyanus sauri 3-Habib bn Abi sabit 4-Abu wa’il 5-Abu hayyaj Asadi. Dangane da maruwaici na farko kuwa abin da Ahmad bn Hambal wanda malamin hadisi ne yana cewa dangane da shi ya wadatar da mu inda yake cewa: Waki yayi kuskure a cikin hadisai guda 500, [80]Sannan ya cigaba da cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi da ma’ana (ba tare da kiyaye lafuzzan da aka yi amfani da su ba) Sannan ba shi da cikakkiyar masaniya a harshen larabci. [81] Dangane da maruwaici na biyu kuwa (Sufyanu sauri) Ibn hajar Askalani ya ambace shi da cewa yana yin "Tadlis"a cikin hadisi. An ruwaito daga Ibn Mubarak cewa, Sufyanus Sauri ya kasance yana ruwaito hadisi yana yin "Tadlis"a lokacin da na iso sai ya ji kunya a Dangane da maruwaici na uku kuwa, Habib bn abi Sabit, Ibn Hibban ya ruwaito daga Ata yana cewa: Ya kasance yana tadlis a cikin hadisi, don haka ba a bin hadisinsa, [84] Amma mai ruwaya na hudu kuwa, wato Abu wa’il wanda sunan shi Shakik bn Salma Asadi Kufi, ya kasance abokin adawar Ali bn Abi Dalib ne, Ibn Abil Hadid yana cewa: Ya kasance daga cikin masu sabani da Imam Ali (A.S) Lokacin da aka tambaye shi Ali kake so ko Usman, Sai ya ce: wani lokaci na kasance Ali amma yanzu Usman.[85] Sai dangane da maruwaici na biyar wato Abu Hayyaj Asadi wanda sunansa Hayyan bin Husain, Tirmizi yana kauce wa ruwaito hadisi daga gare shi, haka nan Ingantattun littattafan hadisai guda biyar ban da wannan ruwayar ba su ruwaito komai daga gare shi. [86] B- Dangane Da Ma’anar Wannan Hadisi Dangane da kirkirar wannan hadisi na Abu hayyaj kuwa kamar yadda muka gani a sama a fili yake abin, domin kuwa maruwaita wannan hadisi ta yadda ake tuhumar su yin tadlis da kuskure wajen ruwaya. Saboda haka ba za a iya dogara da shi ba wajen kafa dalili na shari’a. Koda an runtse ido daga raunata maruwaita wannan hadisi, ma’anarsa ba tabbatar da wannan ma’ana. Saboda haka: domin bayyanar da wannan al’amari ta hanyar bayyanar da wasu kalmomin don fahimtar ma’anar wannan hadisi. 1-" 2-"Illa sawwaitahu"
|