Hikimar Ziyarar KaburburaIdan muka dauki wannan ma’ana dogaron Ibn Taimiyya yana iya zama dai-dai. Amma tare da lura da yadda tarihin musulmai ya tafi a Na farko kamar yadda muka gani a cikin hadisin da ya gabata, ana iya tsammanin wata ma’ana daban, sakamakon wannan ma’ana kuwa ba za a samu wani fito na fito ba a hadisai da ayoyi da kuma tarihin musulmi da suke nuni a Haka nan idan muka dauki ma’ana ta biyu wato muka dauka cewa ai a nan ana nufin "wuri" wato bai halitta ba mutum ya tafi wani wuri sai wadannan wurare guda uku, wannann kuwa zai bayar da ma’anar da ba ta dace ba, sannan fitowar wannan kalma daga mai hikima musamman Manzo ba zai yiwu ba. Wato ya zama an hana zuwa kowane wuri sai wadannan wurare guda uku (Masallacin ka’aba, Kudus da Masallacin Manzo). alhalin musulunci ya halatta wasu tafiye-tafiye da dama a cikin musulunci wasu daga cikinsu ma mustahabbi ne. Misali kamar tafiya domin neman ilimi, ko tafiya domin kasuwanci ko tafiya don sada zumunci, tafiya don yawon bude ido, tafiya domin jihadi da dai sauran tafiye-tafiye da suke halas wadansu ma mustahabbi a musulunci. Saboda haka a nan dole ne mu dauki ma’ana ta farko wato masallaci, cewa kada mutum ya yi tafiya domin ya je wani masallaci sai masallatai guda uku, domin kuwa su ne su kafi sauran masallatai matsayi. Da wannan ne zamu fitar da batun tafiya domin ziyarar Manzo domin ba ita ake magana ba a cikin wannan hadisi. Bayan dangane da ingancin wannan hadisi koda an dauki ma’ana ta farko, akwai shakku a cikinsa. Domin kuwa yana nufin wannan magana ta fito daga bakin Manzo inda take nuni da cewa tafiya zuwa kowane masallaci ba ta inganta sai masallatai guda uku. Alhali kuwa ruwayoyi sun zo a Ziyarar Masallatai Guda Bakwai A sassa daban-daban na garin Madina akwai wasu masallatai guda bakwai wadanda mahajjata sukan ziyarta yayin da suka je Madina, Idan ma muka kara da (masallacin Raddi shams, da na Bilal da na Ijaba) Yawansu zai wuce bakwai. Mahajjata suka yi salla raka’a biyu a wadannan masallatai musamman sukan fi ba da muhimmanci a Amsar wannan tambaya kuwa a fili take: Tafiya domin ziyarar wadannan msallatai ba wai don yazo a cikin shari’a ba ne, ko kuma yin salla a cikin wadannan masallatai yana da wani fifiko na musamman, sam ba haka ba ne manufar tafiya zuwa wadannan wurare sai daya daga cikin biyu ne kamar haka:
|