Hikimar Ziyarar Kaburbura



 Saboda haka da ikon Allah a nan gaba zamu yi magana a kan kiyaye wadannan wurare masu tsarki.

Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)

 Ziyarar Kabarin dukkan musulmi da musamman ziyarar kabarin Manzo wani abu ne wanda yake mustahabbi mai karfi a cikin musulunci. Sannan malaman hadisi daga Sunna da Shi’a sun ruwaito hadisai da dama a kan mustahabbancin ziyarar kabarin Manzo wadanda wasu daga cikinsu sun gabata a cikin bahasin da ya gabata ta yadda babu wani malami daga cikin malaman musuluncin da ya ba kansa damar yin shakku a kan mustahabbancin ziyarar Manzo. Wannan kuwa ya hada har da Muhammad bn Abduh wanda yake da wasu masatlolin dangane da abin da ya shafi annabawa, a nan ba kawai ya yi shiru ba ne, sai dai ya yi magana a kan mustahabbcin ziyarar Manzo (S.A.W). Sannan mun kawo abin da yake cewa dangane da hakan a bahasimmu na baya.

 Tare da la’akari da kasantuwar mustahabbicn ziyarar Manzo, amma msulmi sun kasu a kan wannan kyauta ta ubangiji:

1-Mazauna Madina

Mazauna Madina sakamakon makwautaka da suke da ita da Manzo (S.A.W). Suna iya ziyartarsa ba tare wata wahala ba don aiwatar da wannan mustahabbi.

2-Mazauna sauran wurare a cikin duniya

Mazauna sauran sassan duniya dole ne su yi tafiya domin su damar yin sallama ga kabarin Manzo Su ce: "Amincin Allah ya tabbata a gareka ya manzon Allah".

 A nan tambaya ita ce; menene hukuncin wannan tafiya a shari’a?

Jawabain wannan tambaya kuwa a fili yake domin wannan amsa tana matsayin gabatarwa ce domin aiwatar da aikin mustahabbi, saboda haka a akidar wasu malamai tana matsayin mustahabbi, wasu kuwa suna cewa tana hukuncin halal "Mubah" ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next