Hikimar Ziyarar Kaburbura



  Haka nan ziyartar kaburburan Shahidai wadanda suka bayar da jininsu domin kare al’ummarsu da addinin Allah shi ma yana da matsayi na musamman wanda ya fi na sauran mutanen da ba su ba.

 Ziyartar kaburburan shahidai wadanda suka rasa rayukansu a kan tafarkin ubangiji, bayan tasirin da yake ga ruhin mutum, sannan yana nuna rikon alkawari a kan tafarkin da suka bayar da jininsu a kai. Wato mai ziyara kamar yana cewa ne yana nan kan tafarkinsu sannan zai yi kariya a kan wannan abin mai tsarki da suka bayar da jininsu. Domin mu kara fahimtar abin da kyau bari mu ba da wani misali wanda yake raye a halin yanzu:

 Mutumin da ya ziyarci Dakin Allah, kafin ya yi dawafi yakan yi wa Hajrul Aswad sallama kuma ya sanya hannu ya shafe shi da ma’anar cewa yana yin bai’a ne ga Annabi Ibrahim (A.S) gwarzon tauhidi, da nufin cewa tauhidi shi ne abu na gaba a wajensa. Ta yadda zai yi iya kokarinsa wajen yada shi, amma tunda yanzu ba zai iya kai hannunsa ba zuwa ga Annabi Ibrahim ta yadda zai yi masa bai’a wajen daukar alkari domin wannan aiki shi ne sai ya kai hannunsa ga abin da shi Annabi Ibrahim (A.S) ya bari ta yadda zai gabatar da bai’arsa ta hanyar wannan abin da ya bari. Ya zo a cikin hadisi cewa yayin da mutum yake mika hannunsa zuwa ga Hajrul Aswad yana cewa ne: â€‌Na mika amana da alwakarin da na dauka, sannan na jaddada bai’ata ka sheda a kan hakanâ€‌.[3]

 Ziyartar shahidan Badar da Uhud da Karbala da sauran masoyan da suka bayar da jininsu a tafarkin Allah yana bayyanar da wannan al’amari. Masu ziyarar wadannan wurare masu tsarki sukan yi wa masu wannan wuri sallama da mika gaisuwa zuwa ga ruhinsu tsarkaka, sannan suna daukar alkawari ne a kan cigaba da hanyarsu.

 Da wani kalamin muna iya cewa ziyarar kabarin wani nau’i ne na girmama su. Sakamakon an kashe shahidi a kan wani abu mai tsarki da yake girmamawa, duk wanda ya ziyarci shahidi ya girmama shi, a hakikanin gaskiya ya girmama wannan akidar ne wadda a kanta ne aka kashe shi, sannan yana daukar kansa wanda yake biyayya akan wannan hanya.

Ziyarar Kabarin Manzo (S.A.W)

 Ziyarar Kabrin Manzo mai girma (S.A.W) ko kuma wasiyyinsa mai tsarki (A.S) yana da matsayin hukuncin yi musu bai’a ne bayan nuna girmama su a kan abin da suka yi na sadaukar da rayukan su wajen shiryar da al’umma zuwa ga hanyar Allah da yake nunawa. Imami na takwas wato wasiyyin Annabi kuma halifansa da ya yi wasiyya da shi imam Ridha (A.S) a cikin maganganunsa dangane da ziyarar kaburburan ma’asumai (A.S) yana cewa: Kowane Imami yana da alkawari tsakaninsa da mabiyansa ziyarar kabarin Imamai daya daga cikin wannan alkawarin neâ€‌.[4]

 A hakikanin gaskiya yayin da mutum yake ziyartar kabarin manzo (S.A.W) ko na Imamai kamar yana yin bai’a da alkawari da su ne cewa ba zai taba bin wata hanya ba a cikin rayuwarsa sai hanyar da suka bari.

 Ga abin da mai ziyar kabarin manzo yake cewa: Idan Muhajirun da Ansar wadanda suka halarci yakin Hudaibiyya sun yi maka baiâ€کa a kan kariya ga addini (Fathi: 18).

Sannan idan matan Makka sun yi maka bai’a a kan gujewa daga yin shirka da sabon Allah (Mumtahna: 12).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next