Akidojin ImamiyyaDalilan shari’a su ne: Alkur’ani mai girma, da Sunna, da Ijma’i, da Hankali kamar yadda yake dalla-dalla a littattafan Usulul Fikhi. Samun matsayin Ijtihadi kuwa yana bukatar sani mai yawa da ilimi wandanda ba sa samuwa sai ga wanda ya dage ya yi kokari ya cire nauye-nauyen da suke a kansa ya bayar da kokarinsa domin samunsa. 4- Bayani Kan Mujtahidi Abin da muka yi imani da shi game da mujtahidi wanda ya cika sharudda cewa shi wakilin Imami (A.S) ne a halin boyuwarsa, kuma mai hukunci, shugaba cikakke, abin da yake ga Imami (A.S) na koma wa zuwa gareshi a al’amura da hukunci a tsakanin mutane yana gare shi kuma duk wanda ya ya yi raddi gareshi tamkar mai raddi ne ga Imam (A.S) wanda kuma ya yi wa imami raddi to ya yi wa Allah, wannan kuma yana matsayin shirka da Allah ne kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Sadik (A.S). Shi Mujtahidin da ya cika sharruda ba wai makoma ba ne na mutane a fatawa kawai ba, a’a yana da jagoranci na gaba daya, sai a koma zuwa gare shi a hukunci da raba gardama da shari’a, wannan duk yana daga cikin abubuwan da suka kebance shi, bai halatta ba ga wani ya dauki nauyinsu sai da izininsa, kamar yadda bai halatta ba a yi haddi ko ladadtarwa sai da umarninsa da hukuncinsa. Kuma ana komawa gare shi a kan dukiyoyin da suke hakkokin Imam ne da suka kebance shi. Wannan matsayin ko shugabanci na gaba daya imami ne ya bayar da shi ga Mujtahidin da ya cika sharudda domin ya zama wakilinsa mai maye gurbinsa a lokacin fakuwarsa, shi ya sa ma ake cewa da shi “Na’ibin Imamâ€. FASALI NA FARKO 5- Imaninmu Game Da Ubangiji Madaukakin
|