Akidojin ImamiyyaDaga abubuwan da suka kamata mu jawo hankali gare Shi a wannan koyarwa Shi ne ba a wajabta wa mai ziyara sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba, a’a sai dai ya sanya mafi kyawun abin da zai iya, domin ba kowa ne zai iya yin haka ba, kuma akwai takurawa ga talakawa al’amarin da tausayawa ba ta bukatar a yi haka, sai ya zamanto ya hada tsakanin wannan tarbiyya da abin da ya kamata na kawa da kuma kiyaye halin talaka da mai raunin hali. 3- Ya sanya turare matukar yana da shi, wannan fa’idarsa tamkar ta sanya sababbin tufafi ce. 4- Ya yi sadaka ga fakirai da abin da ya saukaka gare Shi, kuma fa’idar sadaka a irin wannan al’amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimaka wa gajiyayyu da kuma karfafa ruhin tausasawa gare su. 5- Ya tafi yana mai nutsuwa da kwanciyar hankali mai runtse ganin idonsa. Abin da ke cikin wannan irin natsuwar na girmama alfarmar wannan gurin da kuma wanda ake ziyarta da fuskanta zuwa ga Allah (S.W.T) da yankewa zuwa gare shi, ba boyayye ba ne, tare da abin da hakan ya kunsa na nesantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munanawa sashensu ga sashe. 6- Ya yi kabbara da fadin: “Allahu Akbar†ya yi ta maimaitawa yadda ya so, kuma a wasu ziyarorin an kayyade kabbarorin zuwa dari. Akwai fa’idar jin rai ga girman Allah a cikin yin haka, da kuma cewa ziyara ba komai ba ce sai bauta ga Allah da girmama shi da tsarkake shi ta hanyar raya alamomin Allah da karfafa Addinin shi. 7- Bayan kammala ziyarar ga Annabi ko ga Imami sai ya yi salla raka’a biyu a mafi karanci domin bauta ga Allah domin godiya gareshi saboda dacen da ya yi masa ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar. A cikin addu’ar da aka ruwaito wacce mai ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abin da zai fahimtar da mai ziyarar cewa wannan sallar tasa da aikinsa duk don Allah ne shi kadai da kuma cewa Shi ba ya bauta wa wanins, ziyarar ba wata abu ba ce sai wani nau’in neman kusanci zuwa gareShi madaukaki. “Ya Uabangiji gareka na yi salla, gare ka na yi ruku’u, gareka na yi sujada, kai kadai ba ka da abokin tarayya, domin salla da ruku’u da sujada ba sa kasancewa sai gareka, domin kai hakika kai ne Allah babu abin bautawa sai kai. Ya Uabangiji ka yi tsira da aminci ga Muhammad da Zuriyar Muhammad (S.A.W) kuma ka karbi ziyarata, ka kuma ba ni abin da na roka, domin Muhammad da Zuriyarsa masu tsarki.†A cikin irin wannan nau’in na ladabi akwai abin da yake bayyana wa wanda yake son fahimtar hakikanin manufofin Imamai (A.S) da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar kaburbura, da kuma abin da yake toshe bakin masu nuna jahilta da suke raya cewa ziyarar kaburbura ibada ce gare su da neman kusanci gare su kuma shirka ce da Allah. Abin zato a nan shi ne cewa hadafin wadannan shi ne nesantar da jama’a daga abin da yake jawowa jama’ar imamiyya amfanin zamantakewa da na addini a bukukuwan ziyara, domin ya zama tsakuwar ido ga masu kiyayya da Ahlul Baiti (A.S), in ko ba haka ba ba ma tsammanin wadannan mutane suna jahiltar hakikanin manufar Ahlul Baiti (A.S), mustahili ne ga wadannan da suka tsarkake niyyarsu ga Allah suka kadaitu da ibada suka bayar da rayukansu wajan taimakon addini su kira mutane zuwa ga shirka da Allah. 8- Daga ladubban ziyara akwai cewa: Mai ziyara ya lizimci kyautata abotakar wanda yake tare da shi, da karanta magana sai dai da alheri, da yawaita ambaton Allah, da kaskan da kai, da yawaita salla, da salati da runtse idandunansa, kuma ya taimaka wa mabukata daga cikin yan’uwansa idan ya ga guzirinsu sun yanke, da taimaka musu, da tsantseni kan abin da aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayya[42]. Sannan hakikanin ziyara ba komai ba ne sai salati ga Annabi (S.A.W) da Alayensa da la’akarin cewa “Su rayayyu ne ana arzuta su gun Ubangijinsuâ€. Kuma suna jin magana suna amsawa, kuma ya isa ya ce: Assalamu alaika ya RasulalLah! Sai dai abin da ya fi ya karanta abin da aka rawaito na hadisai da suka zo game da ziyara daga Ahlul Baiti (A.S) saboda abin da yake cikinta na daga manufofi madaukaka da fa’idoji na addini, tare da balagarta da fasaharta, da kuma abin da yake cikinta na daga addu’o’i madaukaka da mutum yake fuskanta zuwa ga Allah makadaici a cikinta.
|