Akidojin ImamiyyaNa biyu: Shar’anta ta kuma ya zo a Alkur’ni mai girma, da fadarsa madaukaki: “Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imaniâ€. Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariyaâ€. Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye Imaninsa Ya ceâ€. Surar Gafir: 28. FASALI NA HUDU Tarbiyyar Ahlul Bait Shimfida: Ahlul Baiti (AS) sun sani tun tuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba kuma su da shi’arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa. Don haka a bisa dabi’a suka riki “takiyya†a Addini da dabi’a garesu da su da mabiyansu matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ba ko Addini, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS). Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari’ar Musulunci da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama’a mai amfani domin su zama misalai na musulmi na gari mai adalci.
|