Akidojin ImamiyyaYa ce: Shin yana kan abin da kake kai? Na ce: Na’am. Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin. Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi? Ya ce: Na’am. Abbana ya ce: Sai na tafi, bayan nan –wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kale ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba? Na ce: Haka ne! Ya ce: “Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin! Na ce[56]: hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abbana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.
|