Akidojin ImamiyyaAmma Shahidi Imam Husain (AS) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (S.A.W). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa cika umarni da biyayya ga Imamai (A.S)[50]. A nan kwadayin Ahlul Baiti (A.S) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne, a matakin Imam Zainul Abidin (A.S) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyaka†wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muharnmad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuriâ€. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.†Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsayin addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u da kuma shirya kansu da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jahadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya da nesantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa. Haka nan sauran imamai (A.S) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri da kuma azabtar da su da dukkan nau’in na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su ya yin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyawa da wasunsu bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa su kansu. Ya isa garemu mu karanta wasiyyar Imam Musa Alkazim (AS) ga shi’arsa: “Kada ku kaskantar da kawukanku da barin biyyyar shugabanku, idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah wanzuwarsa, idan kuwa ya kasance azzalumi to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma shugaba adali yana matsayin uba mai rahama ne, ku so masa abin da kuke so wa kanku kuma ku ki masa abin da kuke ki wa kankuâ€[51]. Wannan ita ce matukar abin da ake siffantawa na kiyayewar al’umma ga amincin shugaba da su so masa abin da suke so wa kansu su ki masa abin da suke ki wa kansu. Bayan duk wannan muna cewa: Alhakin shi’a da wasu marubuta na wannan zamani suke dauka girmama! Yayin da suke siffanta shi’a da cewa ita kungiya ce ta asiri mai barna ko kuma wata jama’a ce ta ‘yan juyin juya hali. Haka ne cewa wajibi ne a kan mabiyin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ya ki zalunci da azzalumai da fasikai, ya yi duba zuwa ga mataimakansu duba na kyama da rashin yarda da wulakanci, wannan dabi’a ba ta gushe ba suna gadonta jikoki da ‘ya’ya amma sam ba ya daga dabi’arsu su yi yaudara ko cin amana, kuma ba tafarkinsu ba ne yin juyin juya hali su yi tawaye a kan jagorancin da yake an kafa shi da sunan musulunci, ko a boye ko a sarari. kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko afka wa musulmi ko wace irin Mazhaba ko Darika yake bi, wannan kuwa domin rikoinsu ne da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), kuma duk musulmin da ya yi kalmar shahada biyu a wajansu dukiyarsa da jininsa kubutattu ne, kuma cin mutuncinsa haramun ne; “Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai da son ransaâ€. Musulmi dan’uwan musulmi ne, kuma yana da hakkoki a kansa kamar yadda bahasi mai zuwa zai yi bayaniâ€. 42- Hakkin Musulmi Kan Musulmi Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne ‘Yan’uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne sakacinsu wajan riko da wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci.
|