Akidojin ImamiyyaKo yaya dai Raja’a ba tana daga cikin shika-shikan Musulunci ba ce da ya wajaba a kudurce ta da yin bincike a kanta, imaninmu da ita bi ne ga hadisai ingantattu da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) wadanda muka yi Imani da kubutarsu daga karya, kuma tana daga cikin al’amuran gaibi da suka ba da labari game da ita kuma aukuwarta ba mustahili ba ne. 33- Bayanin Takiyya An ruwaito daga Imamus Sadik (A.S) a sahihin hadisi cewa: “Takiyya Addinina ce kuma Addinin iyayena ce†da kuma “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shiâ€. Haka nan takiyya ta kasance taken Ahlul Baiti (A.S) wajen kare kai daga cutar da su da kuma mabiyansu da kare jininsu da kawo gyara ga halin da musulmi ke ciki da kuma hada kansu. Takiyya ba ta gushe ba a matsayin alama da ake sanin shi’a da ita tsakanin sauran bangarori na al’ummu kuma dukkan mutum idan ya ga alamun hatsari ga ransa ko ga dukiyarsa saboda yarda da abin da ya yi imani da shi ko kuma bayyanar da shi a sarari, to babu makawa ya boye ya kiyaye a guraren hatsarin, wannan kuwa abu ne da dabi’ar hankali ke hukunci da shi. Kuma sannanen abu ne cewa Shi’a da lmamansu sun sha nau’o’in jarrabawa da matsa lamba na tsawon zamani da babu wata jama’a da ta sha irinta. Wannan al’amari ya tilasta su a mafi yawan lokutansu su yi amfani da takiyya suna masu boye wa masu sabani da su, da kuma barin bayyanarwa da suturta akidunsa da ayyukan da suka kebanta da su saboda abin da yake biyo bayan hakan na daga cutuwa a addini da duniya, wannan shi ne ya sanya suka bambanta da takiyya aka kuma san su daita. Takiyya tana da hukunce-hukunce ta fuskacin wajabcinta da rashin wajabcinta daidai gwargwado sassabawar wuraren tsoron cutuwa da aka ambata a babobinta a littattafan fikihu. Ita ba wajiba ba ce a kowane hali, takan iya zama hall ko saba mata ya zama wajabi ne a wasu halaye, kamar idan bayyana gaskiya da fitowa da ita sarari ya zama taimako ne ga Addinin da hidima ga Musulunci da jihadi a tafarkinsa, to a wannan hali dukiya ba komai ba ce kuma ba za a fifita rai ba. Takiyya tana iya zama haram a ayyukan da sukan iya kaiwa ga kashe rayuka masu alfarma ko yada karya, ko barna a Addini, ko cutarwa mai tsanani a kan musulmi ta hanyar batar da su ko kuma yada zalunci da ketare haddi a tsakaninsu. A kowane hali dai takiyya a gun Shi’a ba ta mayar da su wata kungiyar asiri ba ce domin aiwatar da rushe-rushe da ruguje-ruguje kamar yadda wasu daga cikin makiyan Shi’a marasa fahimtar al’amura kamar yadda suke, suke surantawa kuma suka ki dora wa kansu nauyin fahimtar ra’ayi ingantacce. Kamar yadda ba ta sanya Addini da hukunce-hukuncensa sun zama wani sirri daga asiran da bai halatta a bayyana su ga wanda ba ya imani da su ba, al’amarin bai zama haka alhalin littattafan mazhabar Imamiyya da rubuce-rubucensu na fikihu da hukunce-hukunce da bahasosin Akida sun cika gabas da yamma sun ma wuce yadda ake tsammani daga kowace al’umma da take da wani addini. Akidarmu ta takiyya wadanda suke son aibata shi’a sun samu damar amfani da ita, suka sanya ta daga abubuwan da suke sukan su da ita, kamar dai sa iya kashe kishirwar gabarsu sai da fille wuyayensu da takubba da tumbuke asalinsu gaba dayansu a wadancan zamunan da suka gabata da ya isa a ce wannan dan shi’a ne ya gamu da ajalinsa a hannun makiyan Ahlul Baiti (A.S) na daga Umayyawa da Abbasawa har da Usmaniyawa. ldan sukan mai son suka ya dogara ne da abin da yake raya rashin shar’ancinsa a addini, to mu sa mu ce masa: Na Farko: Mu masu biyayya ne ga Imamanmu (A.S) kuma muna bin shiriyarsu ne, kuma su ne suka umarce mu da ita suka wajabta ta a kanmu a lokacin bukata, ita tana daga Addini a wajensu kuma ka ji fadin Imamus Sadik (A.S) da yake cewa: “Duk wanda babu takiyya gare shi babu Addini gare Shi.†Na biyu: Shar’anta ta kuma ya zo a Alkur’ni mai girma, da fadarsa madaukaki: “Sai dai wanda aka tilasta shi alhalin zuciyarsa kuwa tana nutse da imaniâ€. Surar Nahli: 106. Wannan aya ta sauka ne game da Ammar Dan Yasir da ya fake da bayyana kafirci saboda tsoron makiyan Musulunci. Da kuma fadinsa madaukaki: “Sai dai in kuka ji tsoron su don kariyaâ€. Surar Ali Imran: 28. Da kuma fadinsa: “Kuma wani mutum daga mutanen fir’auna yana mai boye Imaninsa Ya ceâ€. Surar Gafir: 28.
|