Akidojin Imamiyya Sannan shi ma ya yi wasiyya da Imamancin Imam Hasan da Imam Husain (AS), shi kuma Husain (A.S) ya yi wasiyya da imamancin dansa Aliyyu Zainul Abidin (AS) haka nan dai Imami ke bayar da wasiyyar imamin da zai zo bayansa har zuwa kan na karshensu kamar yadda zai zo. 30- Adadin Imamai Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamancin gaskiya su ne makomarmu a cikin hukunce-hukuncen shari’a wadanda Annabi (S.A.W) ya yi wasiyya da su da sunayensu gaba daya, sannan wanda yake gabata yana wasiyya da mai biye masa kamar haka:
|