Akidojin Imamiyya



 

23- Bayanin Imamanci

Mun yi imani cewa Imamanci yana daga cikin Usuluddin wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su, kuma bai halatta a yi takalidi da iyaye da dangi da malamai a cikinta ba komai girmansu da darajarsu kuwa, abin da yake wajibi shi ne a nemi sani a yi bincike a game da shi kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.

Atakaice sauke nauyin da yake kan baligi da aka wajabta masa ya dogara ne a kan imani da imamanci tabbatarwa ko korewa, koda mun kaddar cewa imamanci ba ya cikin shika-shikan addini da ba ya halatta a yi takalidi a cikinsu, duk da haka ya wajaba a yi imani da ita ta fuskacin cewa sauke nauyin da Allah ya dora wa baligi –karbar ayyukansa- ya wajaba a hankalce, kuma dukkaninsu ba ba sanannu ba ne ta hanya tabbatacciya yankakkiya, saboda haka wajibi ne muka wa wanda muka san mun sauke nauyin da yake kanmu ta hanyar biyayya gareshi, ko ya zamanto imami (A.S) a mazhabar imamiyya ko waninsa a wasu mazhabobin.

Kamar yadda muak yi imani da cewa annabci tausasawa ce daga Allah, kuma ba makawa a kowane zamani ya kasance akwai imami mai shiryarwa da zai maye gurbin annabi a ayyukansa na shiryar da ‘yan Adam da dora su a kan abin da yake maslaha a Sa’adar duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancance ta, domin tafi da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da ketare iya daga tsakaninsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni shi ne yake wajabta sanya Imami bayan Manzo (S.A.W).

Saboda haka ne muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata. Imamanci ba zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al’amarinsu ba ne da idan suka so zasu nada wanda suka son nadawa ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan ba tare da Imami ba. Ya zo cewa: “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya” kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a Hadisi ingantacce.

Akan haka bai halatta ba wani zamani daga zamanoni ya kasance ba tare da imami ba da yake wajibi a yi masa biyayya wanda yake ayyananne daga Allah (S.W.T) shin mutane sun ki ko ba su ki ba, sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, yana rayuwa a cikinsu ne ko kuwa yana boye ne daga idandunan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya boyu daga ganin mutane kamar yadda ya boyu a cikin kogo da shinge haka na yake game da imami (A.S), kuma a hankalce babu bambanci tsakanin gajeriyar boyuwa ko mai tsayi[32].

Madaukakin sarki ya ce:

“Kuma ga kowace a’lumma akwai mai shiryarwa”. Surar Ra’ad: 8.

“Kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya zamanto a cikinta”. Surar Fatir: 22.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next