Akidojin ImamiyyaHafiz Muhammad Kano Nigeria Asabar: 11 Shawwal 1424 H.K 15 Azar 1382 H.SH 6 Disemba 2003 M 1-Sani Kan Samuwar Allah Mun yi imanin cewa saboda baiwar da Allah ya yi mana ta karfin tunani da kuma kyautar hankali, to ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Za mu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya neâ€. Surar Fussilat: 53 Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai baâ€. (Surar Bakara: 170)
|