Akidojin Imamiyya



4- Abu Abdullah (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da za mu kawo wasu kamar haka:

A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseni”.

B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahama”.

C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni shi ba ya daga cikin masoyanmu”.

D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa kokarinsa ya tsananta kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa ya kaunaci ladansa ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar.

 

38- Munin Zalunci

Ketare haddin wani da zaluntar mutane suna daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (AS) suke girmama muninsa, wannan kuma bi ne ga abin da Kur’ani ya zo da shi na daga tsoratarwa game da zalunci da munana shi, kamar fadinsa madaukaki: “Kada ka tsammaci Allah mai sha’afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna zasu fiffito”. (Surar Ibrahim: 42)

Hakika abin da yake kai matukar bayyana munin zalunci da kyamar sa ya zo a maganganun Amirul Muminin Ali Dan Abi Talib (AS) kamar fadinsa shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga a Nahjul balagha huduba ta 219: “Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha’irin da ta jawo ba zan aikata ba”. Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa.

Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha’ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin mutuncinsu? Yaya za a auna tsakaninsa da aikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayinsa da iliminsa (AS)? Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next