Akidojin ImamiyyaAl’kinani: E. Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina! 4- Abu Abdullah (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da za mu kawo wasu kamar haka: A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseniâ€. B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahamaâ€. C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni shi ba ya daga cikin masoyanmuâ€. D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa kokarinsa ya tsananta kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa ya kaunaci ladansa ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar. 38- Munin Zalunci Ketare haddin wani da zaluntar mutane suna daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (AS) suke girmama muninsa, wannan kuma bi ne ga abin da Kur’ani ya zo da shi na daga tsoratarwa game da zalunci da munana shi, kamar fadinsa madaukaki: “Kada ka tsammaci Allah mai sha’afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna zasu fiffitoâ€. (Surar Ibrahim: 42)
|