Akidojin ImamiyyaDomin mafi karancin koyarwar wannan ‘yanuwatakar ita ce “Ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S). Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi’a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S) za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika su yi riko da wannan dabi’a ta so wa dayansu dan’uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci ko girman kai. Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma’anar hakkin ‘yan’uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga ‘yan Adam sun zama ‘yan’uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki kuma da mafi daukakar sa’adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko ‘yan sanda ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi, kuma da ba su rusuna wa ‘yan mulkin mallaka ba, kuma da dagutai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni’ima kuma gidan sa’ada. Bugu da Karin cewa da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar ‘yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar ‘yan’uwantaka to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma’anar cewa ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa ba, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri da aminci da sa’ada da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya kamar da da dan’uwa sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba. Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma binda ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so ya yi fansa da shi saboda son wani. Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su ita, ita ce ya kasance yana jin hakkin ‘yan’uwantaka ga sauran mutane, to idan kuwa ya kasa wannan to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci da kyautatawa biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T) kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisin imam (A.S) mai zuwa. Saudayawa sha’awar mutum takan yi galaba a kansa sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne ransa ta yarda da akidar adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha’awarsa. Saboda haka ne ma kiyaye hakkin ‘yan’uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan ba shi da imani na gaskiya game da ‘yan’uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa “Al’mu’ula Bn Khunais†bayanin dalla-dallan tambayarsa game da hakkin ‘yan’uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa domin tsoron kada ya koyi abin da ba zai iya aiki da shi ba. Sai Mu’ula ya ce[52]: Menene hakkin musulmi a kan musulmi? Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi. Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?
|