Akidojin Imamiyya



Batun Raja’a kuwa a gurin Ahlussunna yana daga cikin abin ki da imani da shi ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja’a abin suka ga mai ruwaya kuma aibi gare shi wanda yake wajabta kin ruwayarsa da jefar da ita, tayiwu suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka ne ko ma tafi muni, don haka wannan yana daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi’a da shi da aibata su da shi.

Babu shakka wannan wata barazana ce da kungiyoyin Musulmi a tsayin zamani suke amfani da ita domin sukar sashensu, kuma ba mu ga wani abu da zai halatta wannan ba domin imani da Raja’a ba ya rushe imani da tauhidi ko da Annabci, yana ma kara inganta su ne, domin Raja’a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya kamar yadda tashin kiyama da tayar da matattu suke. Raja’a tana daga cikin abubuwan da suka saba wa al’ada wacce ya inganta ta zama mu’ujiza ga Annabinmu Muhammad (S.A.W) da Alayensa. Kuma ita tamkar mu’ujizar raya matattu ce wacca ta kasance ga Annabi Isa (A.S), kai ta fi ta ma domin ita tana kasancewa ne bayan matattun sun zama rididdigaggu. “Ya ce wanene zai raya kasusuwa alhali sun zama rididdigaggu? Ka ce wannan da ya fare su karon farko shi ne zai raya su kuma shi game da dukkan halittu masani ne”. Surar Yasin: 79-87.

Amma wanda ya soki Raja’a kuwa bisa dalilin cewa tana daga cikin “Tanasuhi[38]” wannan saboda shi bai fahimci bambanci tsakanin “Tanasuhi” da tayar da matattu na ainihi ba ne, ita Raja’a wani nau’i ne na tayar da matattu da jikinsu ne, domin ma’anar Tanasuhi ita ce ciratar wata rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba, wannan kuwa ba ita ce ma’anar tayar da matattu na ainihi ba ce, ma’anarsa ita ce komo da ainihin jikin da siffofinsa na kashin kansa da suka kebantu da shi, haka nan ma Raja’a take. Idan kuwa da “Raja’a” “Tanasuhi” ce to raya matattu ta hannun Annabi Isa (A.S) ma ya zama “Tanasuhi” ne, haka ma tayar da matattu da komo da ainihin jikin matattu ya zama “Tanasuhi’’ ke nan.

Saboda haka babu abin da ya rage sai tattaunawa game da “Raja’a” ta fuska biyu.

(1) Na farko: Cewar ita mustahiliya ce.

(2)Na biyu: Karyata hadisan da suka zo game da ita.

(1)A bisa kaddarawar cewa tattaunawar guda biyu daidai ne, to yin imani da ita ba a daukarsa a matsayin kyamar da masu gaba da Shi’a suka mayar da ita, kuma dayawa daga cikin abubuwan da suke mustahilai ne wasu bangarorin musulmi suka yi imani da su ko kuma wadanda sam ingantaccen nassi bai tabbata ba game da su, amma ba su wajabta kafirtawa da fitarwa daga Musulunci ba. Akwai Misalai masu dama a kan hakan kamar: imani da yiwuwar rafkanwa ga Annabi (S.A.W) ko kuma aikata sabo, da kuma imani da rashin farko ga Alkur’ani, da kuma batun narkon azaba, da kuma imani da cewa Annabi bai yi wasiyya ba da halifa a bayansa ba.

Kuma wadannan munakashoshi biyu ba su da wani asasi na inagnci, amma batun cewa raja’a mustahili ce mun riga mun kawo cewa ita nau’i ce na tayar da matattu, sai dai cewa tayarwa ce a nan duniya, kuma dalilin yiwuwar ta shi ne dalili akan yiwuwar tashin kiyama. Kuma babu wani dalili da sai ta zama abin mamaki sai dai kawai ita ba mu saba da ita ba ne a rayuwarmu ta wannan duniya, ba mu san kuma sabubbanta da abubuwan da suke hana ta ba da zasu sanya yin ikrari da ita ko mu kore ta. Tunanin mutum ba ya saukake masa yarda da abin da bai saba da shi ba cikin sauki, kamar wanda yake mamakin tayar da matattu yana mai cewa: “Wanene zai tayar da kasusuwa alhali suna rididdigaggu”. Aka ce masa: “Wanda Ya fare su a tashin farko shi ne zai raya su kuma shi a kan komai masani ne”. (Yasin: 78-79)

Na’am a kan makamancin wannan da ba mu da dalili na hankali akai na tabbatar da shi ko kore shi, ko kuma mu ka raya rashin samuwar dalili to a nan ya zama dole a kanmu mu koma wa nassosin Addini wadanda suke su ne tushen wahayin Ubangiji. Kuma abin da zai tabbatar da yiwuwar Raja’a ga wasu matattu a duniya ya zo a Alku’ani kamar dai mu’ujizar Annabi Isa (AS) ta raya matattu: “Kuma Ina warkar da Wanda aka haifa makaho kuma Ina rayar da matattu da izinin Allah”. Surar Ali Imran: 49. Da kuma fadin Ubangiji: “Ta yaya Allah zai raya wadannan bayan mutuwarsu, sai Allah ya matar da shi Shekara dari sannan ya tayar shi”. Surar Bakara: 259. Da kuma ayar da ta gabata da ke cewa: “Suka ce Ya ubagijinmu Ka matar da mu sau biyu”. Surar Mumin: 11. Ma’anar wannan ayar ba za ta yi daidai ba, ba tare da komowa duniya bayan mutuwa ba duk da wasu daga masu tafsiri sun kallafa wa kawukansu yin tawilin da ba zai kashe kishirwa ba kuma ba zai tabbatar da ma’anar ayar ba.

(2) Tattaunawa ta biyu:- Ita ce da’awar cewa hadisai game da Raja’a kagaggu ne ba ta da asasi, domin Raja’a tana daga cikin al’amuran da suke na larura da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) na hadisai mutawatirai.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next