Akidojin Imamiyya



16- Bayanin Ismar[27] Annabawa

Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma’asumai ne dukkaninsu, haka nan Imamai (A.S), sai dai mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma ga Annabawa ballantana ga Imamai (A.S).

 Isma: lta ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu da kuma kubuta da tsarkaka daga mantuwa koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba, kuma wajibi ne ya tsarkaka hatta daga dukkan abin da yake zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane, ko kuma kyalkyala dariya da sauti mai girma, da dukkan aikin da ake munana yin sa a tsakanin mutane.

Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi shi ne: Da ya halatta ga Annabi ya aikata sabo, ko kuma ya yi kuskure, ko ya yi mantuwa, kuma kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare shi, da sai ya zamanto imma dai ya wajaba a yi masa biyayya a aikin da ya yi na sabo ko kuskure, ko kuwa bai wajaba ba, idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, kai mun wajabta ne ma, wannan kuwa abu ne batacce na larurin Addini da na hankali, idan kuwa biyayya gare shi ba ta wajaba ba a kan haka, to kuwa wannan ya kore Annabcin da babu makawa tana tare da wajabcin biyayya har abada.

Ta kowane hali dai aiki ko zance ya zo daga gareshi da ya zama muna tunanin sabo ne ko kuskure, sai ya zama ba wajibi ba ne a bi shi a cikin kowane abu, sai fa’idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan, sai Annabin ya zama kamar sauran mutane da maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da’iman, kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba, babu kuma nutsuwar zuciya da maganganunsa da ayyukansa baki daya.

Wannan kuwa dalili ne a kan cewa Isma tana tare da Imami, domin kaddarawar cewa shi zababbe ne daga Allah (S.W.T) don shiryar da bayi a matsayin halifan Annabi, kamar yadda zamu yi karin bayani a fasalin Imamanci.

 

17- Siffofin Annabi

Mun yi imani da cewa, kamar yadda ya wa.jaba Annabi ya zamanto ma`asumi, haka nan ya wajaba ya zamanto mai siffantuwa da mafi kamalar siffofin dabi’a da hankali wadanda mafifitan su, su ne jarumtaka, da iya tafiyar da al’amuran mutane, da shugabanci, da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba, da bai inganta ba ya zamanto yana da shugabanci a kan dukkan halittu baki daya ba, ko ya zamanto yana da karfin tafiyar da al’amuran duniya dukkaninta ba.

Haka nan wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya, wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi’u kafin aiko shi saboda zukata su nutsu da shi, rayuka kuma su karkata zuwa gareshi, kuma domin ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 next