Jagorancin Imam Sadik (a.s)bayan hijira, bayan shahadar Imam Hussain bin Ali (a.s). Kamar yanda muka ambata, cikin wannan zangon, al’umma ta kara motsawa kwarai da gaske a fagen manufa (watau aidiyolojiyya) da tinkarar baude-baude ba jirkice-jirkice, wadanda matattarar iko da kuma kwakwalen jahiliyya suka wanzar. Waccar motsawa manufarta gudanar da aiyuka tsawo lokaci domin kafa hukumar musulunci mai tafiya bisa turbar Alkur’ani da sunnar Ma’aiki (s.a.w.a) kamar yanda Imam Ali (a.s) ya misalta. A sarari yake cewa zartarda manhajar sauyi ‘yar asali a cikin al’ummar da ta sami shekaru da dama cikin karkacewar tunani da aiki yana bukatar kwararan dabaru da shiri mai tushe. A wancan lokacin, al’ummar Annabi ta rayu karkashin hukumar Mu’awiya mai cike da karkata gaskiya da musanya ta da wata fuska ta jabu, halin da ya jefa jama’a cikin wani barci mai nauyi tare da nisanta tunanin mutane daga ruhin jagoranci mai bin ka’ida. Wannan baudewa ta kai har lamarin ya janyo kashe badadin Manzon Allah (s.a.w.a) a Karbala, al hali wannan al’umma tana ji tana gani, al’ummar da take fama da halin fargaba da rauni da fatattaka a hannun razanarwar banu Umayya. Saboda haka sai an yi aiki tukuru kafin a iya maido wa wannan al’umma ruhinta rasashshe da mutuntakarta wanda aka tattake, hakika aiki ne mai girma wanda al’umma take bukatarsa domin sake cancantar daukar sakon Islama da kama yunkurin ciccibar nauyin rike shi. Ba makawa ga wani sauyi tamkar wanda Manzon Allah (s.a.w.a) ya fuskanci al’ummar jahiliyya da shi, sannan daga bisani a karbi jagorancin jama’a. Babu shakka dawo da rayuwa irin ta sauyi da sabonta ta aiki ne wanda bai kasa samar da ita tun farko wajen tsauri da muhimmanci ba. Tajdidi irin na juyi yana bukatar imani mai karfi da azama tabbatatta da hankali mai tsarawa da tunani farkakke, wayayye mai motsawa. To wane ne mai daukar wannan nauyin?! Waccar jama’ar da ta kasa tafiya tareda Imam Hassan (a.s) ta kuma kasa kai matsayin taimakawa Imam Hussain (a.s) lallai ba ta iya wannan aikin raya al’ummar musuluncin. Saboda haka dogaro ga wanna jama’ar babu abin da zai haifar illa cin tura da tabewa. Hakika motsin da Tawwabin suka jarraba da tawayen Mukhtar da Ibrahim bin Malik hujja ce babba MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S). Bayan waki’ar Ashura Imam Zainul Abidin Ali bin Hussain (a.s) yana da zabi biyu,su ne:- Imma dai ya sa sahabbansa shiga wata harka sakamakon motsawar rai da tausayi ya jefa su cikin wani garaje wanda wutarsa ba badewa ruruwarta zai yi sanyi, ya bice (saboda ba su da sifofin masu jihadi), sannan daga bisani a bar wa Banu Umayya filin ci gaba da danniya da babakere kan makomar al’umma wajen tunani da siyasa, ko kuma ya rinjayi tausayi da biri---bokon fushi da tunzura, kana ya tanadi share fage wa wani babban aiki wanda zai kai ga dawo da rayuwa irin ta musulunci. Bukatun share fagen su ne tunani mai jagorantan aiki da samar da wata salihar jama’a domin ta zama iri ga juyi da sauyi nan gaba, ya kuma nisanci idanun Banu Umayya, ya ci gaba da aiki haikan wanda manufarsa ita ce gina tunani da kuma dai-daikun matane. Da haka ne zai yi tafiya mai yawa To wani zabi ko hanya zai fifita? Ko shaka babu, hanyar farko ita ce ta sadaukarwa da daukar fansa, sai dai jagoran da yake shiri saboda harakar tarihi da kuma zamanin da tsawonsa ya zarce tsawon rayuwar Imam nesa ba kusa ba, sadaukar da rayuwarsa kawai ba ta isa. Dole ne ya zama mai zurfin tunani, mai yalwar zuciya, mai hangen nesa mai dabara da hikima cikin al’amuransa. Wadannan sharrudda sun wajabtawa Imam zabar hanya ta biyun. Imam Ali bin Hussain (a.s) ya zabi ta biyun duk da dauriya da wahal-halu da juriya da kuncin da ke tattare da wannan hanya. Ya ba da rayuwarsa Imam Sadik (a.s) ya sifanta mana yanayin da imami na hudu ya rayu a kai da kuma rawar da ya taka ta jagaba, ya ce:-“Bayan Imam Hussain (a.s) mutane sun juya baya banda mutum uku, Khalid Alkabuli da Yahya ibn Ummi Dawil da Jubair bin Mud’im. Daga bisani sai mutane suka dawo suka yawaita. Yahaya Ibn Ummi Dawil ya Wannan riwaya tana nuna halin da al’ummar musulmi take ciki bayanan kashe Imam Hussaini (a.s). yanayi ne mai ban tsoro, na fatattaka da raunin zuciya wanda ya game al’ummar musulunci a lokacin da waccan waki’ar ta faru, abin takaicinda ya auku a
|