Jagorancin Imam Sadik (a.s)Wajibi ne mai binciken tarinin musulunci ya yi tambaya Amsa a’a, bisa dabi’a wannan ba zai yiwu ba. Gagarumar farfa-gandar da mulkin Umayyawa suka dana ta hanyar daruruwan alkalai da hakimai da masu huduba ba za ta rushe kuma ta ci tura ba idan ba wani zayyanannar farfaganda mai hamayya da waccar, wacce wani tsari hadadde, daidaitacce, boyayye ya yunkura da ita ba. Dab da mutuwar Mu’awiya aikace-aikacen wanna shirin Alawiyyawan ya ci gaba, saurinsa kuma ya karu. Lamarin ya kai ga hakimin Madina ya rubuta wa Mu’awiya abin da ya kunshi wannan: “Bayan haka, Umar ibn Usman (dan leken asirin hakimin Madina wanda ya sa ido kan Imam Hussain (a.s)) ya ba mu labarni cewa wadansu mazaje daga Irak da sashen manyan mutanen Hijaz suna yawan zuwa wajen Hussain Ibn Ali, suna kuma tattauna batun daga tutar tawaye …….ku rubuto mana ra’ayin ku.â€[46] Bayan waki’ar Dabari ya ce : mutanen basu rabu da tara kayan yaki da shirya masa da kiran jama’ar shi’a da ma waninsu, a asirce, Abin da littafin Jihadu Shi’a yake fadi gaskiya ne, inda ya yi taliki wa zancen Dabari da cewa:- “Bayan kashe Imam Hussaini, jama’ar shi’a ta bayyana a matsayin wata jama’a mai tsari, ra ayoyin addini da alakar siyasa suna dinke ta, tana gudanar da tarraki tana da shugabanni, kana tana da karfin soji. Jama’ar “Tawwabun†ita ce farkon mai bayyana dukkan wanna. Bincike kan al’amuran da suka auku a tarihi da ra’ayin marubuta tarihin kan wancan zamani, ga alama, yana nuna cewa shi’a suna daukar nauyin jagoranci da shirye-shirye, sai dai farajiyar fusata da sukar Banu Umayya ta fi tsararriyar jama’ar shi’an nan fadi. Wannan farfajiyar tana haduwa da kowace haraka mai rinin shi’a . Za mu gane cewa masu motsawa da hamayya kan Banu Umayya ko da sun yi amfani da taken shi’a ba dai dai ne mu dauka cewa dukkansu suna cikin adadin shi’a ba, watau adadin tsararren shirin nan na imaman Ahlulbaiti (a.s) Bayan bayanin da ya gabata, ina son in yi ta’akidi kan cewa bayan shahadar imam Hussaini wadanda kadai ake kiransu shi’a su ne jama’ar nan da take da alaka mai karfi da imamin gaskiya, tamkar yanda lamarin yake a zamanin Amirul Muminina (a.s). Wannan jama’a ita ce bayan sulhun Imam Hassan (a.s) ta fuskanci kafa tsarin shi’a da umarnin Imam, kuma ita ce ta yi kokarin jawo mutane zuwa wannan tsarin da kuma kange mafiya yawa wadanda basu kai matuka a tunani ba kuma basu yi kwari a fagen aiki ba balle su kai matsayin shiga tsarin, wanda yake da zimmar samar da wata babbar harakar shi’a. Riwayar da muka kawo a farkon wannan bahasi wacce aka rawaito daga Imam Sadik (a.s) mai cewa adadin muminai bayan waki’ar Ashura bai wuce uku ko biyar ba, abin da take nufi shi ne ‘yan wannan kebantacciyar jama’a. watau mutanen nan da suke iya rawar gani, a matsayinsu na madugu mai wayewar kai a kokarin kaiwa matuka cikin al’amarin juyin Alawiyyawa.
|