Jagorancin Imam Sadik (a.s)



Yanayin tunani da zamantakewa mai kaskanta mutane ya zaburar da Imam da mabiyansa wajen haraka mai dorewa ba tare da gajiya ko kosawa ba domin sauya wannan mummunan yanayi da tabbatar da  abinda Ubangiji ya wajabta na kawar da wannan baudiyar.

Suna ganin mafiya yawan mutane sun rusna wa gurbatanccen yanayin da Banu Umayya  suka yada, suka nitse cikin kazantar abin duniya iya wuya har suka wayi gari tamkar mahukuntan nasu,basu fahimtar zance, kunnensu bai jin nasiha. “Idan mum kira su ba sa amsa mana”.[14]

Ta wata fuska kuwa, Imam da jama’arsa suna ganin bincike-binciken fikihu da ilmul kalam da hadisi da tafsiri na karkata ne wajen dadada wa  fir’aunancin Umayyawa da bin sonransu. Saboda haka duk hanyoyin dawowar jama’a kan katari da sun toshe, ba don zaburar mazhabin Ahlulbaiti wajen bayar da wajibinsa ba  idan kuwa muka kyale su ba za su shiriya ta hanyar waninmu ba[15]

Mazhabin Ahlulbaiti ya yi Allah wadai da malamai da mawaka da suka sayarda kansu. An yi wannan sukan ne saboda kokarin farkarda   zukatan wadancan malaman ko kuma zukatan mabiyansu. Imam yana fadawa Kumait, sha’irin Ahlulbaiti, da lafazin suka:- yabon Abdulmalik kayi?

Ya ce:- Ban ce da shi ‘ya shugaban shiriya’ ba, abin da na ce shi ne ‘ya zaki’ zaki kuma kare ne, ‘ya rana’ rana kuwa jamadatu ce, ‘ya kogi’ kogi kuwa mataccen abu ne, ‘ya maciji’ maciji kuwa kwaro ne mai wari, ‘ya tsauni’ tsauni kuwa kurman dutse ne. Sai Imam ya yi murmushi. Kumait sai ya rera wannan baitin gaban Imam:-

 Zuciyar da so ya tsare ya aure?

                                     Ban da yaranta tasa har da guri,

Wannan mimiyar ta kafa mararraba tsakanin alkiblar Alawiyya  da ta Umawiyya a daraja da kuma halaye ta hanyar dawwamammar zaiyanawa mai kyan gaske.

Wata rana Ikrima almajirin ibn Abbas wanda yake sananne ne, mai matsayin ilmi a cikin al’ummar wancan zamanin ya je yin mukabala da Imam sai haibarsa da natsuwarsa da ruhinsa da tunaninsa suka kama Ikrima. Abin da kadai ya iya fada shi ne:- “Ya dan Manzon Allah hakika na zauna gaban Ibn Abbas da waninsa sau da yawa amma irin abin da ya same ni yanzu bai taba samu na ba”. Sai Imam ya amsa masa da cewa:- “(Kai kana gaba ga gidaje wadanda Allah ya yi wa daukaka kuma ake ambaton sunansa a cikinsu)[16]

Ta wandansu fuskoki daban na ayyukan mazhabin Ahlulbaiti a wannan zangon kuwa, akwai jerin zalunci da fir’aunanci da kisa da azabtarwa da kora, da suka kewaye Ahlulbaitin Manzon Allah da mabiyansu ba don komai ba sai domin kokarin da suke yi na iza matacciyar zuciyar mutane da girgiza rayukansu wadanda suka yi sanyi da zaburar da kwantacciyar azamarsu da shiryar  da su zuwa harakar juyi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 next