Jagorancin Imam Sadik (a.s)1.Akwai wata tsararrar alaka ta tunani da ta abin da ya shafi dukiya tsakanin imamai (a.s) da mabiyansu, kuma an kasance ana daukar dukiyoyi daga sassa dabam dabam na duniya ana kaiwa Madina kazalika da tambayoyin addini mayawaita. 2.Fadadar fagen da ke wilaya ga mutanen gidan Manzo (s.a.w.a) musamman a yankunan duniyar musulunci wadanda suke masu saurin daukar dumi. 3.Tattaruwar jama’a masana hadisi da maruwaita Kurasanawa da Sistanawa da Kufawa da Basarawa da Yamanawa da Misrawa gaban Imam (a.s). Shin wannan al’amari wanda sashensa yake munasaba da sajewa da sashe ya faru ne kwatsam ba tare da an shirya shi ba? Wajibi ne mu yi kari da cewa wannan al’amari ya tabbata ne karkashin ikon siyasa wanda ya yi da gaske wajen watsi hatta da sunan Ali (a.s) kai da ma zagin Ali a Idan da ace masu kiran Ahlulbaiti suna takaita bayanansu ne A nan tambaya za ta zo Duk da haka riwayoyin da suke fayyacewa gwargwado Wani mutum daga mutanen Kufa ya zo Kurasan, sai ya kira mutane zuwa wilayar Jafar ibn Muhammad (a.s). Wata jama’a sai ta bi shi ta amsa kiransa. wata kuma ta musa masa ta yi inkari wata kuma ta dakata ta yi tsantseni. Sannan riyawar ta ce: Sai mutum daya daga kowace jama’a ya tafo wa Imam Abu Abdillahi (a.s). Mai magana daga cikinsu shi ne wannan da ya dakata ya yi tsantsenin. Sai ya ce : Allah ya kiyaye ka, wani mutum ya zo mana daga mutanen Kufa ya kira mutane zuwa biyayya da wilaya gare ka sai wasu mutane suka amsa masa, wasu suka yi inkari wasu kuma suka ya tsantseni suka dakata. Imam (a.s) ya ce:- “Daga cikin ukun wacce kake ciki? “Ya ce:- Daga jama’ar da ta yi tsantseni ta dakata. Ya ce: To ina tsantsenin ka yake daren kaza da kaza? (sai ya tunatar da shi kasawarsa a wani hali na sha’awa) sai mutumin ya yi shakka. [35] Kamar yanda ka ji, mai kiran daga mutane Kufa yake, kiran nasa kuwa zuwa imamancin Ja’afar ibn Muhammad Al Sadik (a.s) da wilayarsa da kuma biyayya gare shi ne.
|