Jagorancin Imam Sadik (a.s)Kafin mu bijiro da hujjoji Kalmomin da aka tsago daga ita kalmar ‘imama’kamar su ‘imam’ da ‘a’imma,’ duk inda suke a cikin Alkur’ani abin da ake nufi da su shi ne kebantaciyar ma’anarsu watau jagorancin al’umma. A wadansu wurare abin da ake nufi da ita shi ne jagorancin tunani a wadansu kuwa jagorancin siyasa ko kuma biyun gaba daya. Bayan kaurar Ma’aiki da bayyanar rarrabuwar salon tunani da siyasa tsakanin jama’ar musulmi, A makarantar Ahlulbaiti, wacce mabiyanta suke ganin kansu a matsayin ma’abota ra’ayin tunanin musulunci mafi tsabta, ita ma tana daukar Imami ko kuma shugaban siyasa a al’ummar musulunci dole ne ya zama abin nadawa daga Allah ta hanyar sanarwa daga Annabi. Dole ne ya zama jagora a tsarin tunani, mai fasssarar Alkur’ani , masanin dukkan mas’alolin addini masu zurfi da rikitarwa (daka’ik)da kuma alamu irin na ramzi a cikin addini. Wajibi ne ya zama ma’asumi wanda aka kubutar daga duk wani aibi na halitta ko dabi’u ko aibin da taliki yake janyo wa kansa. Wajibi ne ya zama ya fito ne daga tsatso mai tsarki da tsabta. Saboda wannan a fahimtar musulunci na karnin farko da na biyu imamanci na dauke da ma’anar jagorancin siyasa, a fahimtar mabiya Ahlulbaiti a kebe kuwa, Saboda haka manufar imamanci wajen mabiya Ahlulbaiti tana komawa ga yanda imami ko shugaban al’umma yake bayar da misalin jagorancin al’umma ta hanyar rayuwarsa cikin jama’a da kuma yanda yake hulda da dai-daikun mutane. Imami shi ne madugu a tafiyar, shi yake koyarwa da tarbiyyantarwa kuma shi ne jagoran gudanar da rayuwa. Idan mun lura da wannan to Annabi (s.a.w.a) shi ma imam ne saboda shi ne jagoran tunani da siyasa na al’ummar da ya kafa ginshikanta. Bayan Annabi, al’umma tana bukatar wani imami ya gaje shi ya dauki kayan nauye-nauyen da suka rataya a wuyarsa, a cikinsu kuwa akwai nauyi na siyasa. Shi’a suna imani da cewa Annabi ya yi furuci da nassi Ya zama wajibi mu yi ishara da cewa shiga junan nauye-nauyen nan uku na imamanci watau jagorancin siyasa da koyar da addini da tarbiyyar dabi’u da ruhi wadanda musulunci ya sifantu da su, sun samo asali ne daga rashin rabewa tsakanin wadannan sassa uku a shirin da musulunci ya tanadar wa rayuwar bil Adama. Jagorancin al’umma dole ne ya hada da jagorantarta a wadannan fagage uku. Saboda wannan fadi da halin tattarau na manufar imamanci a wajen shi’a, ba makawa nadin imami ya zama daga Allah subhanahu wa ta’ala. Muna iya tsamowa daga abin da ya gabata cewa imamanci, sabanin yanda ma’abota biri-bokon ra’ayi suke gani, ba manufa ce wacce ake kwatantawa da ‘halifanci’ ko ‘hukuma’ ko wani matsayi wanda ya takaita da al’amuran ma’anawiyya da ruhi da tunani ba, a’a, shi, a tunanin shi’a, jagorancin al’umma ne a al’amuran addininta da abinda ya danganci hakan kamar tsara rayuwa a yanayin zaman jama’a da na siyasa ( shugaban kasa). Kazalika imamanci shi ne kula da sha’anin koyarwa da shiryarwa da kuma fuskantarwa a al’amuran wa’anawiyya da ruhi da warware matsalolin tunani da manufar (aidiyolojiyya) musulunci (jagorancin tunani). Abin takaici, wannan bayyanannar mas’ala ta zama bakuwa a zakatan mafiya yawan masu akidar imamanci. Domin haka muna ganin ya zama dole mu kawo wasu misalai daga daruruwan hujjoji na Alkur’ani da hadisi a
|